Tuesday, 15 September 2020
Dr Muhammad Rabiu R/lemo Yayi Martani Mai zafi kan masu Kona Kudi

Home Dr Muhammad Rabiu R/lemo Yayi Martani Mai zafi kan masu Kona Kudi
Ku Tura A Social MediaAlhamdulillahi dr sheikh Muhammad Rabiu R/lemo wanda yake dalibi ga Dr Sheikh Muhammad sani umar R/lemo kuma zaman kane ga Dr yayi martani ga masu koda kudi , saboda banbancin siyasa ko fusatattun matasa da wannan abun yazo a yayin da wani mawakin siyasa ya nuna yana so a tura masa da kudi.

Dr Muhammad Rabiu Rijiyar lemu yayi wannan jawabi a shafinsa na sada zumunta wanda Hausaloaded na kawo muku bata kara ba ,ko rage abinda malam yace ba.

Ga jawabinsa.

"Sabawa Allah ne kona kudi, saboda Allah ya hana tozarta dukiya, kamar yadda Manzon Allah S.A.W ya fada a cikin hadisi. 

Haka nan almubazzaranci ne yin hakan. Allah kuwa ya fada mana a Alkur'ani mai girma cewa masu almubazzaranci yan uwan shaidanu ne.

Duk wanda ya kona kudi ya tuba zuwa ga Allah, ya sani Allah yana iya jarrabarsa ya hana shi ko kobo, ya toshe masa kofofin arziki, don bai girmama ni'imar da Allah ya yi masa ba.

Ba wa mabukata kudi da tallafa musu shi ne abin da Allah yake so, ba ba wa wani mawaki ba.

Allah ya shiryar da mu gaba daya."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: