Labarai

BABBAR NASARA: ‘Yan Sanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 15 Da Cafke 50 A Katsina (Hotuna)

…Sun kama bindigu kirar Ak 47 tara da kirar gida 20 da tsabar kudi miliyan shida

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin Kwamishinan yan sanda, Alhaji Sanusi Buba, sun yi nasarar kama barayin shanu da yan fashi da makami da masu satar mutane a jihar Katsina cikin wata ukku da suka wuce.

Kwamishinan yan sanda na jihar Katsina, ya bayyana haka lokacin da ya ke baje-kolin masu laifi a helkwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina.

Alhaji Sanusi Buba ya bayyana cewa rundunar yan sanda ta jihar ta yi nasarar cafke masu aikata miyagun laifuka, wanda ya hada barayin shanu da yan bindiga masu satar mutane da masu kashe kashe a yankuna daban daban na jihar Katsina da kuma masu fashi da makami guda hamsin. An samu bindigogi kirar Ak 47 guda tara da kuma kirar gida guda ashirin da mashinan hawa guda ashirin da kuma shanu guda dari biyu da ashirin, wadanda suka sata. An kuma samu tsabar kudi har naira miliyan shidda.

Kwamishinan yan sanda ya cigaba da cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta yi nasarar kashe yan bindiga goma sha biyar har lahira kuma sun ceto wadanda suka sace guda ashirin daga hannun su.

Sanusi Buba ya ce rundunar ta yi nasarar cafke masu aika fyade guda dari da arbain, yanzu haka an maka wadanda suka aikata fyade guda tamanin da bakwai da ke gaban kuliya a kotuna daban daban na jihar Katsina

Daga karshe Kwamishinan yan sanda, Alhaji Sanusi Buba ya mika godiyar sa ga sauran jamian tsaro da suke aiki a jihar Katsina, na irin goyan bayan da suke ba rundunar, har ta kai ga wannan gagarumar nasara da muka samu. Har ila yau, ya mika godiyarsa masu rike da sarautun gargajiya da alumma Jihar Katsina na irin hadin kai wajen ba da bayanan sirri. Rundunar ta ba da tabbacin cewa za ta kawo karshen masu aikata miyagun laifuka a jihar Katsina.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button