Uncategorized

Amfanin 11 da ruwan ganyen itacen gwaiba ke yi a jikin mutum da wasu illolin sa 3

BI AISHA YUSUFU

Wani likita mai suna Dr Ademola ya yi kira ga mutane da a rika dafa ganyen gwaiba ana shan ruwan sa kamar shayi akai-akai cewa yin haka na inganta kiwon lafiyar mutum.

Ademola ya ce banda haka shan jikon ruwan ganyen itacen gwaiba na kara karfin gaban namiji.

Dalla-Dalla a nan:

1. Rage kiba – Shan ruwan ganyen itacen gwaiba na taimaka wa mutum wajen rage kiba a jiki.

2. Yawaita Shan dafaffen ruwan ganyen itacen gwaiba na kare mutum daga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya.

3. Dafa ganyen Itacen gwaiba da karas na kara karfin gaban namiji a lokacin saduwa.

4. Ruwan ganyen itacen gwaiba na kwawar da cutar siga wati ‘Dibeties’.

5. Yana taimakawa wajen kaifafa kwakwalwar mutum.

6. Ganyen gwaiba na kare mutum daga kamuwa da cutar daji.

7. Yana taimakawa wajen kawar da ciwon ciki, atini da gudawa.

8. Ganyen gwaiba idana aka hada shi da mai yana inganta kyan fatar mutum.

9. Yana Kara tsawon gashi.

10. Yana taimakawa wajen samun barci musamman ga wadanda ke fama da rashin yin barci da dare.

11. Ganyen gwaiba na inganta karfin garkuwar jikin mutum domin daidai da mura ganyen na kawar da shi.

12. Yana maganin ciwon hakori Idan ana yawan kuskure baki da ruwan kuma yana kawar da warin baki.

Likitan ya ce amfani da ganyen gwaiba ta hanyoyin da bai kamata ba na cutar da kiwon lafiyar mutum. Ya Yi Kira ga mutane da su tabbatar sun dafa ganyen gwaiba kafin su sha ruwan domin guje wa matsaloli.

Ga wasu matsalolin da ka iya faruwa idan aka yi amfani da ganyen gwaiba ta hanyar da bai kamata ba.

1. Kada a bai wa mai ciki ruwan ganyen gwaiba ta sha domin haka na iya cutar da ita da dan dake cikin ta.

2. Kada a hada maganin bature da ruwan gwaiba a sha.

3. Yawaita shan ruwan gwaiba na hana abinci narkewa a cikin mutum a sha shi sannu sannu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button