Labarai

Yanzu – Yanzu : Obaseki ya cire rufin Majalisar Dokokin Edo

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da ke kudancin Najeriya ya cire duka rufin majalisar dokokin jihar da zimmar hana kowa zama cikin ginin majalisar.
Wannan na zuwa ne bayan da ‘yan sanda a jihar suka yi wa ginin majalisar jihar kawanya wadda ke Benin babban birni jihar.
Kakakin gwamnan Obaseki ya shaida wa BBC cewa ya yi hakan ne da nufin hana wasu ‘yan siyasa ciki har da gwamnan wata jiha cika burinsu na kwace jihar lokacin da ake daf da gudanar da zaben gwamna a jihar.
Gwamman jami’an tsaro ne suka sanya shinge a wajen ginin majalisar.
Kakakin ‘yan sandan jihar Chidi Nwabuzor ya bayyana cewa jami’an sun je ne da nufin kare rikicin da ake zaton zai iya tashi.
Rikicin siyasa na kara ƙamari a jihar da aka tsara yin zaben gwamna a watan Satumbar gobe.
Rahotanni sun ce babu dai kowa a cikin ginin majalisar. Kimanin mutum 200 ne suka yi carko-carko a wajen ginin majalisar, kuma mafi yawansu magoya bayan gwamna mai ci ne.
Al’amura na kara rikicewa tun bayan tuɓe mataimakin kakakin majalisar Yekini Idaiye da aka yi a ranar Laraba kan zargin shi da karya doka.
A baya ya fito ƙarara ya nuna goyon bayansa ga abokin hamayyar gwamna mai ci.

A sauya shekar da yayi na ban mamaki a watan Yuni, Gwamna Godwin Obaseki, ya sauya daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa babbar jam’iyyar hamayya ta Bbchausa.com na ruwaito
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button