Kannywood

Yadda Mu Ka Yi Rabon Tallafin Gidauniyata A Kannywood – Rashida Maisa’a

Kamar yadda ta saba a tsawon lokaci ta na talafa wa mabukata, Gidauniyar Maisa’a Charity Foundation a yanzu ma ta kara fadada tallafin da ta ke bayarwa a wajen mabukata.

Kodayake babu wani lokaci da a ke ganin Gidauniyar, wadda ke kakashin kulawar Rashinda Adamu Abdullahi, ta fi bayar da tallafi kamar a watan azumin da ya gabata a lokacin da a na tsaka da zaman gida, wanda cutar Korona ta haddasa.
A kan haka ne LEADERSHIP A YAU ta ji ta bakin Hajiya Rashidan dangane da yadda  ta gudanar da rabon kayan tallafin da kuma irin jan damarar da ta yi, don ganin jama’a sun samu saukin rayuwa, inda ta fara yi ma na bayani da cewar,
To ka san shi wannan yanayi da a ka shiga wata annoba ce da ta hada duniya baki daya, wanda mu dai tun da mu ka taso ba mu taba ganin irin wannan jarrabawar ba.

“Kuma alhamdulillahi wannan gidauniya ta yi iya yin ta saboda mun bi lungu da sako kofa zuwa kofa, don kai wa jama’a kayan tallafi, kuma gaskiya wannan abin da mu ka yi akwai wadda mu ka shiga gidanta muka ajiye ma ta buhun shinkafa sai da gabanta ya fadi, ni har tsorata na yi, kamar za ta suma matar nan.

“Mu na tunanin yadda za mu raba abincin, don kada a daka wawa, amma da ya ke mun tafi da jami’an tsaro haka mu ka yi rabon cikin tsari, kuma zan iya cewa abin ya amfanar sai godiya ga Allah na yi abin iya karfina na nema a wajen hukumomi da daidakun mutane inda muka samu buhun shinkafa dari uku, to kuma dai abin da ya kara ma na farin ciki lokacin da mu ke aikin rabawa sai wasu masu bukatar taimakawa da su ka gani suka rinka taro ma na kamar akwai kwamishinan kananan hukumomi na Jihar Kano Murtala Sulen Garo, ya kira mu ya ba mu kayan abinci da suga.
“Sannan akwai dan Majalisa Sha’aban Ibrahim Sharada shi ma ya bayar da tasa gudunmawar, don tallafawa mabukata, wanda mu ka raba har cikin ‘yan fim ma, don mutane da dama a cikin masana’antar fim sama da 1,500 su ka amfana da abincin da ya ba mu.

Kuma gaskiya rabon abincin da na yi a cikin ‘yan fim gaskiya na ji dadinsa, domin akwai wasu tsofaffin ‘yan fim da na dade ban gan su ba, don ban yi tunanin ma su na raye ba, amma lokacin da mu ka yi wannan rabon kayan abincin duk sun rinka zuwa su na karba.

“Tun daga kan Ali Nuhu zuwa kasa babu wanda bai amfana da kayan tallafin da na raba ba. Mun bai wa daraktoci irin su Aminu Saira, Kamal S. Alkali, ka ga kamar Ibrahim Danko na fi shekara biyar ban gan shi ba, sai a lokacin, su Husaini Sule koki, su Isa Bello Ja, su Nakwango, kai duk jaruman nan babu wanda ban kira na ba shi kayan tallafin ba.
“Kuma alhamdulillahi mutane sun ji dadi sosai, don shi Ibrahim Danko saboda ya ji dadin abin har waka ya yi kuma na ji dadin sosai ka san an ce yaba kyauta tukuici. To a dai masana’antar fim ‘yan kadan ne wanda ba su samu ba, don har wadanda su ka mutu mun kai gidansu, kamar irin su Ibro da Ubale Wanke-wanke duk an kai wa iyalansu.

“Gaskiya na ji dadi duk da cewar kowacce shekara ina yin rabon kayan abinci, amma a wannan shekarar mun kirawo mutanen da ba su san za mu kirawo su ba sun zo sun karbi kayan tallafin, kuma za mu cigaba da yin wannan aikin har zuwa karshen rayuwarmu da yardar Allah.”

A yayin da wakilinmu ya tambaye shirin da ta ke yi domin kara fadada ayyukanki na rabon kayan tallafi, sai ta ce, “to, shiri da ma kullum a cikinsa mu ke, kuma wannan zaman na Korona da a ka yi da kuma yadda muka shiga cikin al’umma ya sa na kara fahimtar jama’a suna bykatar tallafi don haka ne ma a yanzu na kara jan damara domin ganin aikin da nake yi ya cigaba, domin ni da ma tun da na taso a rayuwata mai sha’awar taimakawa jama’a ce da haka na tashi don haka na ke so na kasance cikin taimakon jama’a har zuwa karshen rayuwata, domin babu lokacin da na fi jin dadi kamar lokacin d ana ga wani ya na cikin tsananin bukatar taimakon na ga na samu mafita daga cikin halin da na ke ciki, wannan abin ya na saka ni cikin farin ciki da jin dadi.”

A karshe Hajiya Maisa’a ta ce, “Ina kira ga jama’a su bada karfi wajen taimaka wa jama’a daidai iyawarsu. Kuma taimakon jama’a fa ba sai mai kudi ba, da dan abin da Allah ya hore ma ka za ka iya yi, domin idan ka na ganin wani ya fi ka, to kai ma ka fi wani. Don haka sai ka tallafa wa na kasa da kai. Ina fatan Allah ya taimake mu ya kara rufa ma na asiri.”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button