Labarai

Shugaba Buhari Ka Tuna Haduwarka Da Allah ~ Datti Assalafy

Gwamna Zulum na jihar Borno ya fada maka gaskiyar abinda yake faruwa a jiharsa game da wadanda suke cin amanar tsaron kasa, ya rage gareka a matsayinka na shugaban kasa ka koresu ka hadasu da EFCC ko kuma ka barsu su cigaba da cin amanar da ka basu

Amma a matsayina na cikakken masoyinka da nake fatan ka samu tsira ba wai anan duniya ba har a lahira mu rayu cikin Aljannah, ya kamata ka rabu da mutanen nan maciya amana, domin sun gaza, sai karya kawai da kama karya, rayukan talakawanka na salwanta, babu wanda ya tsira

Shugaba Buhari idan baka fahimci cewa suna cin amanarka ba to Maigirma gwamnan jihar Borno ya fada maka gaskiya, idan ka sani ka kyalesu to ka sani Allah ba zai barka ba, akwai hisabi

Idan tsafi suka yi gareka wanda yayi tasiri a kanka ta yadda ba zaka taba ganin cin amanar da suke maka ba to Allah Ya karya sihirin, ya bayyana maka su a matsayin cikakkun maciya amanar Kasa ka koresu

Shugaba Buhari Allah Ya sa ka wanye lafiya Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button