Wasanni

Paul Pogba Ya Kamu Da Cutar Korona

Dan wasan Mancheter United Paul Pogba ya kamu da korona, in ji kocin ƙungiyar kwallon kafa ta Faransa Didier Deschamps.

A halin yanzu, dan wasan mai shekara 27 zai killace kansa na kwana 14.

Bbchausa ta ruwaito,ba zai buga wasan da Faransa za ta buga ba da ƙungiyar kasar Sweden a ranar Asabar 5 ga watan Satumba, da kuma wasan gida da za ta buga bayan kwana uku da Croatia.

Sai dai Pogba zai iya buga wasan farko na Premier da kungiyarsa Manchester United za ta kara da Crystal Palace a filin wasa na Old Trafford a ranar 19 ga watan Satumba.

Kungiyar tasa ta ce: “Kowa a kungiyar na yi wa Pogba fatan samun sauƙi gabanin fara sabuwar kakar wasanni ta bana.”

Matashin ɗan wasan kungiyar Rennes mai shekarar 17 Eduardo Camavinga ne zai maye gurbin Pogba.

“Na sauya tsarin ƴan wasan kungiyata da za su buga wasan a kan lokaci,” in ji koci Deschamps.

Ya kuma ce, “an yi rashin sa’a Paul Pogba ya kamu da cutar korona bayan sakamakon gwajin da aka yi masa ya fito a safiyar yau.”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comRelated Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button