Saturday, 1 August 2020
Ni na kawo rawa da waka a cikin masana'antar fina-finai - Lilisko

Home Ni na kawo rawa da waka a cikin masana'antar fina-finai - Lilisko
Ku Tura A Social Media
A cikin fina-finan da a ka yi a shekarun baya a Kannywood, duk fim din da ka gani an shirya rawa da waka ta bada ma'ana to ko shakka babu Lilisko ne ya shirya ta, domin kuwa an yi zamanin da duk cikin masana'antar fina-finai ta Kannywood, shi kadai a ke ji da shi a fagen shirya rawa da waka. Sai dai duk da sauyin zamani, har yanzu Shu'aibu Idris Lilisko ya na nan a na damawa da shi a cikin harkar, domin haka mu ka nemi jin ta bakin sa, domin ya fadawa ma su bibiyar mu halin da ya ke ciki a yanzu.

Ya kuma fara da cewar "To Alhamdulillahi har yanzu mu na cikin harkar a na damawa da mu, sai dai ba kamar yadda a ka sammu ba a baya, saboda lokacin ya sauya, amma a can baya yawanci idan an ce Shu'aibu Idris Lilisko, an san shi wajen koyar da raye-raye, domin haka duk wani fim da za a zo da shi a wancan lokacin mu za a nema na zo na fitar da tsarin raye-rayen da za a yi na al'ada na Gargajiya, hatta na zamanin ma, a wannan lokacin, ni zan fitar kuma ni zan tsara. To kuma har ta kai ta kawo lokacin ya na ja har a ka zo zamani da kuma girma ya na zuwa, a nan na ga ya kamata mu bar matasan yara da su ka shigo su ma su ci gaba da yi, kamar yadda a da mu ma mu ka dorar mu ke yi. Ko ba komai duk wanda ya san harkar rawa ta Gargajiya da ma ta zamani a cikin masana'antar nan ya san ni na fara kirkirar ta, domin haka ni na kawo rawa da waka a cikin masana'antar fina-finai ta Kannywood, domin haka yanzu mun bar wa matasa, ko da za mu yi to yanzu ba za mu yi irin wancan ba sai dai wani abu daban, domin haka sai mu ka zama ma su bayar da shawarwari a kan yadda ya kamata a yi".

Ya ci gaba da cewa"A yanzu na koma fitowa a matsayin jarumi kawai, saboda haka ina matsayin jarumi ne yanzu a harkar fim ba mai yin rawa ko kuma koyar da rawar ba, domin haka ma a yanzu matakin da mutane su ka fi sa ni na da shi, shi ne rol din da na ke fitowa a matsayin Dan sanda ko dai wata fitowa makamanciyar haka, domin haka tun da girma ya zo mana harkar rawa mun barwa yara, amma dai abu ne na ke jin dadin sa tun da ni na samar da shi a cikin harkar, domin haka ina yin alfahari da rawa da waka". Inji Lilisco.

Shu'aibu Lilisko ya kuma yi kira ga matasa Jarumai su rinka yin abun da ya dace domin ganin su ma nan gaba a na tunawa da su.

Share this


Author: verified_user

2 comments: