Kannywood

Na dawo masana’antar Kannywood da karfi na – Jarumi Salisu S Fulani

Daya daga cikin jarumai da su ka dade a na damawa da su a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Salisu S Fulani, ya ce dawowar da ya yi cikin masana’antar Kannywood a wannan lokacin, ya dawo ne ba da niyar doke sauran jarumai ba a Kannywood.

Jarumi Salisu S Fulani ya tabbatar da hakan ne ga wakilin mu a lokacin da su ke tattaunawa da shi dangane da yadda a wanna lokacin a ke ganin sa a cikin Sababbin wakoki da kuma fina-finai, wanda kuma kafin wannan lokacin an dauki lokaci mai tsawo ba a gan shi ba a cikin masana’antar ba.

Cikin tattaunawar da northflix tayi da jarumin ya fara da cewar “Ko a shekarun baya abun da ya sa mutane su ka dai na gani na, saboda yanayi na karatu da na ke yi ne, wanda kuma a yanzu na gama, domin haka na dawo harkar gadan-gadan, saboda ka san komai lokaci ne, kuma Allah ne ya ke juya zamani, domin haka zan iya cewa Allah ne ya yi mini wannan ni’imar ba yin kaina ba ne”.

Dangane da yadda ya samu masana’antar a yanzu kuwa cewa ya yi.

“To zan iya cewa na samu masana’antar a yanzu ta yi kasa ba kamar a baya ba, duk da ya ke dai ba harkar fim ce kadai ta yi kasa ba, kusan duk wasu harkokin kasuwanci haka su ke, amma dai mu fatan mu shi ne Allah ya dawo mana da harkar ta fi ta baya ma. Amma dai duk da haka daga dawowa ta harkar a yanzu ba zan iya cewa ga iya yawan fina-finan da na fito a cikin su ba da kuma wakoki, saboda gaskiya su na da yawa”.
Wakar da a ka fi ganin ka da ka fito a cikin ta ita ce Aure Martaba wadda ku ka yi da Aisha Humaira, wakar fim ce, ko kuma dai kawai an yi ta ne ita kadai ba tare da za a saka ta a cikin fim ba?
“To a yanzu dai waka ce a ka yi, amma dai za a saka ta a cikin fim ne sai dai a yanzu wakar ce ta fita a yanzu haka ma ta na kan YouTube”.
Yanzu harkar fim din Hausa ta koma YouTube ku na ganin hakan zai zama shi ne mafita kuwa?

“To ka san komai lokaci ne, domin yadda zamani ya zo da haka za a karba abun a haka, domin ai ka ga da ba a san za a yi faifan CD ba, kuma zamani ya zo da shi, saboda haka ina gani ba wani abun mamaki ba ne nan gaba ma a samu fasahar da ta fi ta YouTube, fatan mu dai harkar ta ci gaba a duk yadda mu ka samu kan mu. Duk da haka mu na ta kokarin samar da wa su hanyoyin, domin ka ga ai akwai gidajen Talabijin da su ma a ke ba su, duk da dai su ma yanzu harkar ta tsaya, amma dai duk ci gaba ne”.

Ya ka kalli kan ka a matsayin jarumi bayan dawowar ka?

“To gaskiya na ji dadi, musamman ma dai yadda na ga mutane sun karbe ni da wandanda su ka sanni a baya da wadanda ma sai a yanzu su ka fara gani na, to gaskiya babu abun da zan ce sai godiya ga Allah”.

Menene sakon ka na karshe?

“Ni sako na ba zai wuce na yi godiya ga Allah ba, kuma ina kara godiya ga dukkan masoya na da a kullum su ke tare da ni, ina yi wa kowa fatan alheri”. Jarumi Salisu S Fulani.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button