Labarai

Me Yasa Gwamna Zulum Ya Damu Da A Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Gida? shirin Da Ya Kamata Kowa Ya Sani

Rayuwar Mutane a sansanin ‘yan gudun hijira ba alheri bane musamman ga musulmi, amma su makiya zaman lafiyar mu kuma makiya addinin mu suna matukar murna da farin ciki su ga musulmi yana rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira cikin wahala da takuri, da wannan ne zasu samu damar cimma burin su

Abubuwa da suke faruwa a sansanin ‘yan gudun hijira dake kasar Borno babu dadi, kungiyoyin sharri na turawa sun zo da sunan zasu bada agaji da tallafi amma ta karkashin kasa suna yiwa Musulunci da Musulmai muguwar illa fiye da illar da ‘yan ta’addan Boko Haram suke yiwa Musulunci da Musulmai

A sansanin ‘yan gudun hijira na Borno an raba adadi mai yawa na Musulmai da addininsu sunyi riddah, an lalata tarbiyyan Musulmai maza da mata, an koya musu shaye-shaye da ha’inci da rashin kuna da rayuwa irin na bayahude, ga Luwadi da Madigo, kawalai suna ta cin kasuwarsu a sansanin ‘yan gudun hijiran, zina da ‘yan mata da matan aure ya zama tamkar ruwan dare, wasu sai anyi zina da su kafin su samu abinda zasu ci

Ban sani ba ko kun fara fahimtar dalilan da ya sa gwamna Zulum ya matsu da a mayar da ‘yan gudun hijira garuruwansu?, a hira da BBC Hausa tayi da gwamnan yana cewa rayuwar wahala da akeyi a sansanin ‘yan gudun hijira ya sa wasunsu suna shiga cikin kungiyar Boko Haram, to gaskiya matsalar ta wuce haka, shiga Boko Haram da sauki akan matsalar dake faruwa a sansanin ‘yan gudun hijira

Jama’a ku duba abinda ya faru a Kasar Somalia, kafin ‘yan tawayen Somalia su dauki makami a kafa kungiyar Al-shabab a Somalia Shari’ar Musulunci sukeyi dari bisa dari, kusan kashi 99 na mutanen Somalia musulmai ne, amma me ya faru bayan ‘yan tawaye sun dauki makami aka mayar da miliyoyin mutane sansanin ‘yan gudun hijira?

A lokacin sai da aka wayi gari babu wata hukumar tsaro da take aiki a Somalia, kowa yana rike da bindiga, babu gurin kaiwa kara, Somalia ta koma matattara  na kowani irin ‘dan iska a duniya, har daga nan Nigeria mutum zai aikata mummunan laifi ya gudu Somalia ya buya a can, Kasar ta lalace gaba daya, dubbannin Somaliyawa sun tsallaka turai sunyi riddah, daga kan iyakar turai za’a taresu ace duk wanda yayi ridda za’a barshi ya shige

Duk da wannan; mafi munin barnan da ya faru a Somalia shine mayar da mutane zuwa sansanin ‘yan gudun  hijira (IDP camp) aka ajiyesu, manyan kungiyoyin turawa da na addinin nasara aka basu izni suka je Somalia suka kafa sansani suna taimakon ‘yan gudun hijira, suka gina manyan dakunan bautar addininsu, suka dauko hayar dakarun NATO don su bada kariya na musamman ma wannan dakunan bautar, duk bala’in ‘yan tawaye ba su isa harin wannan gurare ba

Shekara da shekaru miliyoyin Somaliyawa suna rayuwar wahala a sansanin gudun hijira, anan ne aka yiwa Musulunci mafi munin barnan da ba’a taba yin irinsa ba a tarihin Kasar Somalia, don ku gane yadda makircin yake, sai akazo batun cewa a mayar da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu, a boye kuma sai a karfafi ‘yan tawaye a sakar musu da hanya mutane suna komawa gida sai aji anyi hari, saboda ajandar da ake dashi shine ana so dole mutanen nan su dawo sansanin gudun hijira a cigaba da yakar addinin Musulunci, to jama’a wanann shine sak da abinda yake faruwa a Borno, kuma shine makircin da aka shirya a garin Kukawa bayan an bar fararen hula sun koma gida Boko Haram suka bugi garin suka yi garkuwa da daruruwan mata da maza

Jama’ar Musulmi ko kuna da masaniyar cewa kashi 40 cikin 100 na mutanen Somalia yanzu ba Musulmai bane? kun san cewa yanzu a Somalia har da “Satanic Church” wato dakin bautar addinin masu bautar shaidan akwai?, kun san cewa yanzu har da “Free Thinkers” akwai, wato wadanda ba su yarda da samuwar Allah ba, wanda a da Musulmai ne? wanda kafin rikicin Kasar; kashi 99 cikin 100 na mutanen Kasar Musulmai ne, a ina aka rabasu da Musulunci? amsar shine a sansanin ‘yan gudun hijira, wannan ne fa abinda ake so a kawo a Borno

Gwamna Babagana Zulum mai kishin addinin Musulunci ne, ya san sirrin, kuma ya san makircin da yasa aka bar mutanen Borno suke rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira alhali ana da karfin ikon da za’a iya mayar da su garuruwansu, kuma a karesuamma anki, shiyasa hankalinsa a tashe yake, bashi da wani buri da ya wuce a kwashe mutanen nan a mayar da su gidajensu, domin matsalar ta wuce na cewa suna shiga Boko Haram saboda wahala

Kuma ta yanda zaku kara fahimtar cewa makirci ne, shine me yasa idan ‘dan Boko Haram ya ajiye makami ake daukarshi a masa gata, a kaishi kebantaccen guri wai ana canza masa tunani, zuwa wani lokaci a yayeshi a bashi kudade a sallameshi bayan ya gama kashe mutane?, su kuma ‘yan gudun hijira an barsu a sansani cikin tsananin wahala da azaba babu wani kulawa, don haka ajandace wannan da makirci domin a yake mu ta karkashin kasa

Kuma sam bai kamata gwamnonin Arewa Musulmai su kyale gwamna Zulum akan wannan yaki ba shi kadai, Musulunci ake yaka, duk wanda Allah Ya bashi ikon fada aji a wannan gwamnatin bai yi wani yunkurin na ganin an mayar da ‘yan gudun hijira gida ba kuma ya san abinda yake faruwa a sansanin to wallahi yaci amanar Musulunci, kuma sai ya hadu da mummunan sakamako a gurin Allah

Daga bangaren Musulmai maciya amanar tsaro masu karfin ikon da suka ki yarda a mayar da mutane gida daga sansanin gudun hijira saboda kwadayi na neman kudi, ya sa sun kasa fahimtar cewa wa yahudawa suke yiwa aiki ba tare da sun gane ba to su shirya haduwarsu da Allah, kamar yadda nake cewa suma ‘yan Boko Haram da tsageru ‘yan kungiyar Madakhila masu kafirta Malamai da halasta zubar da jininsu wa yahudawa suke yiwa aiki ba tare da sun gane ba

Tabbas irin wannan bayanan makiya basa kaunar ya bayyana, dole a cire tsoro a fito a fadi abinda yake faruwa, domin kamar yadda gwamna Zulum ya fada ne, idan ba’a cire tsoro an fadi gaskiya ba to wannan yakin ba zai taba karewa ba, kowa ya san da wannan

Yaa Allah Ka kawo mana taimako da agaji ta yanda ba muyi tsammani ba Amin Shafin datti Assalafy na ruwaito.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button