Wasanni

Mahaifin Messi Yayi Bala guro Zuwa Manchester City Domin tattauna wa akan Komawar Dansa, Koeman ya ce ba ya buƙatar Suarez a Barcelona

Jaridar Sun ta ruwaito cewa mahaifin Lionel Messi yana Ingila inda yake tattaunawa da Manchester City wacce za ta bai wa dansa kwangilar shekara biyu bayan dan wasan na Argentina, mai shekara 33, ya ce yana son barin Barcelona.bbchauusa na tattara wannan labari
Idan komai ya tafi kamar yadda ake so, City za ta biya £500m kan dan wasan, in ji Telegraph.
Duk kungiyar da ke son daukar Messi za ta biya £90m duk shekara domin ya dace da albashin da ake biyansa a Barcelona(Times – subscription required)
Messi zai halarci atisaye a filin wasan Barcelona ranar Litinindomin guje wa matakin shari’a da kungiyar za ta iya dauka a kansa. (Sport – in Spanish)
Manchester United tana da kudin sayen Messi, sai dai har yanzu tana zawarcin dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, a cewar Express.
Sabon kocinBarcelona Ronald Koeman ya gaya wa dan wasan Uruguay Luis Suarez, mai shekara 33, cewa ya nemi wata kungiyar domin ba ya bukatarsa a Barca. (Mail)
An ba da dama ga dan wasan Bournemouth da Wales David Brooks, mai shekara 23, ya tafi zaman aro kuma akwai yiwuwar Manchester United ta dauko shi idan ta gaza biyan £108m kan Sancho. (Express)
Monacota ki amsa tayinManchester United na biyanta £22m don karbo dan wasan Faransa Benoit Badiashile, mai shekara 19(RMC via Star)
Tottenham na dab da kammala kulla yarjejeniya da Wolverhampton Wanderers don dauko dan wasanta Matt Doherty. Wolves na so a ba ta kusan £20m kan dan wasan mai shekara 28 dan kasar Jamhuriyar Ireland sai dai Tottenham na son biyan kasa da haka. (Independent).
Dan wasanBayern MunichThiago Alcantara ya shirya tsaf domin barin kungiyar. Munich na son a biya ta kusan £30m ka dan wasan kuma an ce Liverpooltanason dauko dan kasar ta Sufaniya mai shekara 29. (Express)
Edinson Cavani ya yi watsi da tayin tafiya Juventus a bazara saboda amanar da ke tsakaninsa da tsohuwar kungiyarsa Napoli. Dan wasan na Uruguay mai shekara 33 ya bar Paris St-Germain a karshen kakar da ta wuce. (Sky Sports Italy, via the Mail)
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comRelated Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button