Zamantakewar Aure

Ma’aurata Zallah : Abubuwa 8 da yin jima’i akai-akai ga mace mai ciki ke yi

Ba tun yanzu ba za ka ji mutane na cewa yin jima’i ga mace mai ciki na kawo wa wannan ciki matsalar gaske wanda ya sa a duk lokacin da mace ta dauki ciki sai ta rika kaurace wa mijinta saboda tsoron kada samu matsala.

Sai dai kuma bincike da dama da aka yi game da hakan ya nuna akasi, cewa ba gaskiya bane cewa mace mai ciki zata iya fadawa cikin hadarin rasa ranta, ko kuma jaririn idan ta cigaba da saduwa da mijinta.

An gano cewa lallai saduwa na kara lafiyar mace da jaririn dake cikin ta.

Ga dalilai 8

1 –  Jima’i na rage wa mace mai ciki yin nakuda mai tsawon wajen haihuwa sannan da rage jinya bayan an haihu.

2 –  Jima’i ga mace mai ciki na kara karfin mara sake hana kuccewar fitsari a lokacin da ko ta yi atishawa, tari ko Kuma a lokacin da ta ke dariya.

3 –  Jima’i na taimakawa wajen kwantar wa mace mai ciki hankali.

4 –  jima’i na rage hauhawar jini da mata’ kanyi fama da shi a lokacin da suke dauke da ciki.

5 –  Yin jima’i ga mai ciki na kawo matukar gamusuwa musamman idan kafin ta dauki cikin tana da matsalar rashin samun ni’imar saduwa

6 –  Jima’i na taimakawa mace saukin nakuda. Idan tayi har lokacin nakuda ya zo, zai zo mata da sauki.

7 –  Jima’i na Kara dankon soyayya dake tsakanin Mata da miji Wanda haka ke da Mata da miji hada hannu wajen rainon Dan da aka haifa.

8 –  Jima’i na rage laulayin ciki da mata kan yi fama da shi.

Julie Revelant ce ta rubuta wannan rahoto da aka wallafa a fox news.

Daga: Sirrin rike miji

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?