Labarai

ISIS da Al-Qaeda ‘sun kutsa yankin arewa maso yammacin Najeriya’

Amurka ta bayyana cewa kungiyar ISIS da Al-Qaeda sun soma kutsawa zuwa yankin arewa maso yammacin Najeriya.
A watannin da suka wuce an samu karuwar hare-hare a Kaduna da Katsina da Sokoto da Zamfara da kuma wasu jihohin yankin.
A taron manema labarai, kwamandan dakarun Amurka na musamman a Afrika, Dagvin Anderson ya kara da cewa kungiyar Al-Qaeda kuma na kara fadada rassanta a yankunnan kasashen yammacin Afrika.
Bayanan wadanda aka wallafa a shafin intanet a ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Anderson y ace Amurka za ta ci gaba da hada gwiwa da Najeriya domin musayar bayanan sirri.
A cewarsa hare-haren Al-Qaeda sun janwo rufe makarantu fiye da 9,000 kuma 3,000 daga ciki a kasashen Mali da Burkina Faso.
“Muna tattaunawa da Najeriya kuma za mu ci gaba musayar bayannan sirri domin kara fahimtar ayyukan masu tsattsaurar ra’ayi,” in ji Anderson.
“Hakan na da matukar mahimmanci gannin yadda kungiyar ta yi barna a jihar Borno kuma a yanzu ta soma samun gindin zama a yankunan arewa maso yammacin Najeriya.”
Gawarwaki a Katsina

BBC
Barnar da ‘yan bindiga suka yi a Batsari

  • 2000Yaran da aka mayar marayu
  • 600Matan da aka kashe wa mazaje
  • 1/3Yawan wadanda suka tsere don gudun hijira
  • 40%Wadanda ba su yi noma ba a bara.

Bayani: Hakimin Batsari

Anderson ya ce idan ana son taimakon kasashen waje yayi tasiri a yaki da ta’addanci a Najeriya dole ne gwamnatin kasar ta shiga sawun gaba wajen murkushe kungiyar.
“A kan batun Najeriya, kasar na da mahimmanci a yammacin Afrika. Akwai bukatar gwamnati ta shiga gaba domin zubarar da yunkurin yaki da kungiyar”.

Garambawul Kan Tsaro

A makon nan ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurnin a yi garambawul ga baki daya tsarin tsaro a ƙasar.
Sai dai da dama daga cikin ‘yan ƙasar na saka ayar tambaya kan me shugaban ƙasar ke nufi da garambawul da kuma manufarsa a wannan karon.
Kuma abin da tambaya shi ne ko wannan garambawul zai yiwu idan hafsoshin tsaro na kan muƙamansu?
Group Captain Sadik Shehu mai sharhi kan al’amuran tsaro a Najeriya ya ce ba ya tunanin cewa ci gaba da zaman manyan hafsoshin sojin kan muƙamin su zai kawo cikas ko kuma wata matsala ga yin wannan garambawul ɗin.
A cewarsa, shugaban ƙasa ke da wuƙa da nama a hannunsa, idan yana so a yi wannan garambawul ɗin ko hafsoshin suna kan muƙaminsu hakan zai yiwu.
Ya ce “soja a dimokradiyya, gaskiya a ce mashi ya je ya yi ne kawai, ko waɗannan mutane suna nan, ko ba su nan za a yi, su an ɗauke su aiki ne.
'Yan gudun hijira a Baratsari

ASALIN HOTON,@SALISU LAWAL FACEBOOK
Bayanan hoto,

‘Yan gudun hijira a harabar fadar Sarkin Ruman Katsina a Batsari
“Idan shugaban ƙasa da ministan tsaro da ma’aikatar ‘yan sanda suka ce ana so a yi wannan garambawul ɗin, a gaskiya zamansu ko rashin zamansu ba zai hana a yi wannan aikin ba.”bbchausa na ruwaito.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button