Wasanni

Ina Matasanmu Masu Barin Sallah Saboda Kallon Kwallo?

 

Daga S-bin Abdallah Sokoto

Akwai wata mugunyar dabi’a da matasanmu ke yi a wannan zamani ta barin sallah cikin lokaci saboda kallon kwallo, yau idan aka ce kungiyar su tana buga wasa da misali karfe 1:10 to a ranar ba zai samu yin sallar azahar cikin lokaci ba, idan ma ba a yi sa’a ba a ranar ko sallar ba zai yi ba, saboda kallon kwallo, alhali babu abinda za ta amfanar da shi duniya da lahira in banda asara.

Yanzu ku duba ku gani, wannan bawan Allah Muhammad Salah kowa ya san cewa shahararren dan wasa ne a duniya, sannan ya tara biliyoyin kudi ta wannan sana’a, sunansa ya zagaya duniya ta sanadin wannan sana’a, amman ji yadda yake riko da addinisa, hatta cikin jirgin sama bai manta da addininsa ba, karatun alqur’ani mai girma yake yi. Amman kai saboda tsabar hauka ka bari har lokacin sallah ya wuce ba ka yi sallah ba kana can wajen kallonsu, alhali babu wata riba da za ka samu duniya da lahira in banda asara.

Ubangiji Allah ka kaddari matasanmu su gane kuskuren yin hakan, sannan ka basu ikon gyarawa tun kafin lokaci ya kure musu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comRelated Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button