Kannywood

GIDAN BADAMASI Ko Asibitin Magance Hawan Jini? Kashi na 2

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
#GidanBadamasiSeason2

Kamar yadda labarin yake, Alhaji Badamasi (Magaji Mijinyawa) wani matsolon attajiri ne, wanda ya yi gwagwarmayar rayuwa ya tara abin duniya. Daga bisani laulayin jiki ya sa yake rayuwa a keken guragu. Ya tara ’ya’ya maza da mata, a sakamakon auri-saki da ya sha yi a rayuwarsa. Kamar yadda ya fada da bakinsa, ya auri mata 12 a rayuwarsa. Ta fannin aiki ko sana’a kuwa, ya ce ya yi dakon giya, ya yi leburanci da sauransu.
Fim din Gidan Badamasi ya ta’allaka ne kacokan kan rayuwar shi Alhaji Badamasi da ta iyalinsa da barorinsa a gida da waje. Duk wani abu da ya wakana a fim din, yana da dangantaka da Badamasi kai tsaye ko a kaikaice.

Jerin ’yan wasan da ke fim din sun dace da guraben da aka zaba masu. Irin yadda Hajiya Zulai (Hajiya Jummai), a matsayinta na uwargidan Alhaji Badasi ta rika tafiyar da al’amuran gidan, ya nuna kwarewarta a wasan barkwanci, duk kuwa da cewa a can baya ba a fina-finan barkwanci take fitowa ba.
Babban yaron gidan Alhaji Badamasi, Taska (Falalu Dorayi), ya taka rawa sosai wajen bayyana halayen yaran gida a gidan attajirai. Ya san yadda ake kulla munafunci, alaye, kamar kuma yadda ya iya mu’amala da maigida da ’ya’yansa masu mabambantan halaye.

A halayen Bazuka (Mustafa Nabaraska), an bayyana wani tantirin dan bariki, wanda ya kware wajen sana’ar holewa. Ita kuwa Sabira (Hauwa ’Yar Auta) ta wakilci irin gaulaye kuma kauyawan matan nan da ke zuwa birni barance. Dankwambo (Nura Dandolo), a matsayinsa na babban dan Alhaji Badamasi da ya shiga duniya, ya wakilci irin tantiran nan da suka buga bariki kuma suka kasa tsinana wa kansu komai. Rayuwarsa na nuna cewa babu nasara ga matashin da ya zabi rayuwar holewa da rakashewa.

A rayuwa da halayen Zaidu (Aminu Mirror), an bayyana mana irin halayen masu fakewa da guzuma suna harbin karsana, masu halayen Annabi Musa a fuska, Fir’auna a zuci. Shi kuwa Adhama (Tijjani Asase), a fim din yana wakiltar irin shashashan mutanen nan da ba su da wani burin ci gaba a rayuwarsu. Ga kato har kato amma bai amfana wa kansa komai, matarsa ke yi masa linzami.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button