Uncategorized

Amfanin Man Kifi Guda (13) Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

Ai sharin Dan Allah Jama’a
1.Man kifi yana karawa zuciya lafiya da rage yawan barazanar kamuwa da cutukan da ke iya shafuwarta.Dalili anan shi ne yana kawarda mugun
cholesterol dake daskare hanyoyin jini daka  
iya haifarda cutar zuciya da makamantansu.
2.Yana rage hauhawan jini.
3.yana kara kaifin tinani da samuwar lafiyar kwakwalwa. Dan haka masu karamcin hankali za a iya basu man kifi.
4.man kifi yana rage nauyin jiki da tumbi.
Za a rinka sha a kiyaye abinci mai kitse da kuma fake ayukkan motsa jiki.
5.Yana da amfani dan
kara lafiyar ido da karfin gani da kauda gani bushi bushi a sanadin karamcin vitamin A.
6.man kifi yana karawa yara karfin jiki da maganin yawan kamuwa da cutuka.
7.man kifi yana maganin kumburin ciki.
8.Man kifi yana maganin ciwon jiki da ga6o6in jiki.
9.Man kifi yana maganin kitsen hanta.
10.Man kifi na gyara fatar jiki sanadin yawan kunar rana a jiki.
11.yana taimakwa mata masu juna biyu Dan samun lafiya da rage yawan laulayi a lokutan ciki.
12.yana kara lafiya da samarda mamma ga mace mai shayarwa.
13.man kifi yana maganin tarin lala.
A kula, zai fi ayi amfani da kifi maimaikon man kifi,amma idan ba za a iya amfani da kifi ba to sai ayi amfani da man kifin,akan sha daidai karfi da lafiyar jiki,ta yanda wata illa ba zata faru ba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button