Kannywood

WATA SABUWA: Ku zama jagora ga cikan burin yaranku ba za ku yi danasani ba, Ali Nuhu ga iyaye

Fitaccen Jarumi a masana’antar Kannywood Ali Nuhu ya ja hankalin iyaye da su zama masu karfafa wa ‘ya’yansu gwiwa tare da taimaka musu  wurin cikan burin su na abin da suke so su zama a rayuwa.

Ali Nuhu ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook da Instagram ayayin da yake jinjinawa fitaccen jarumi kuma mawaki TY Shaban kan yadda ya zama ƙashin baya wurin cimma burin dansa a sana’ar da a zaba. Mawaki mai tasowa Freeboi.

A cewar sa, “Yayi matukar burgeni yadda na ga TY Shaban ke kasancewa ƙashin baya ga cikan burin dansa. Wannan shine abin da ya kamata iyaye su yi, ku zama jagora ga yaranku, daga baya ba za su kauce daga kan hanya, illa su kara maida hankali”.

Ya ci gaba da cewa, “ga duk iyayen da suka yi wa yaransu irin haka, ku sani cewa ba zaku taba yin danasani ba domin yawancin iyaye sun shigar da yaransu sana’ar da suke yi”.

Fitaccen Jarumin ya bada misali da kansa da cewa, “gareni, ‘yata Fatima ta zabi sana’ar kwalliya, sannan dana ya zabi yin Fim da Buga Kwallon kafa kuma a baya ya taba zama Jakadan kamfanin Madara na Blueboat Milk.

Daga karshe ya shawarci iyaye da su taimaka wa yaransu su cimma burin su domin yana sa su kasance masu ƙarfin gwiwa da kuma mai da hankali!

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?