Thursday, 30 July 2020
Shawarwari Masu Tsada Domin Samun Gudanar Da Ibadun Ranar Arafah Cikin Sauki ~ Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Home Shawarwari Masu Tsada Domin Samun Gudanar Da Ibadun Ranar Arafah Cikin Sauki ~ Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Ku Tura A Social Media


Ku taho in nuna muku hanyoyi masu tsada domin ganimantar wannan yini mai Albarka kamar yadda Annabi SAW ya ambata mana falalar sa;

1 Ku yi barci da wuri a Daren da yake kafin yinin arfah;

2 Ku tashi kafin asuba da niyyar yin suhur sabida a shirya ma azumin wannan yini mai tsada;

3 Sannan Ku yi nafilah raka'ah biyu ko hudu a cikin sujjadodin Ku yi addu'a Ku roke ALLÃH alkhairan duniya da lahira Sannan Ku gode ma SA da YA Baku dama kuka kawo wannan rana wacce a cikin ta ake rabon gafara da Alkhairan duniya da lahira a kyauta;

4 Kafin sallar Asuba, Ku dauki wasu lokuta kuna rokon ALLÃH gafara sabida a sanya Ku cikin wadanda suke Neman gafara a cikin dare kamar yadda ayar Suratuz Zhariyat ta bayyana;

5 A je a nemo abinci aci (a matsayin suhur);

6 A yi Raka'atal Fajr;

7 A Shirya ma sallan Asuba  (a tafi masallaci, a yi tahiyyatul masjid, a zauna a cigaba da azkar da tilawan Alqur'ani);

8 A yi sallar Asuba bayan an idar da sallar a zauna a masallaci ko a inda aka
 yi sallah, a cigaba da azhkar da karatun Alqur'ani har zuwa fitowar rana;

9 Ayi sallar walaha raka'a biyu ko hudu minti sha Biyar bayan fitowar rana sabida ka samu ladar aikin hajji da umrah kamar yadda ya tabbata daga Annabi Muhammad SAW. Dan uwa don ALLÃH kada kayi wasa da wannan damar;

10 Bayan nan ka je kayi bacci na Wasu lokuta domin ka kara samun karfi a jikin ka domin ka samu damar karasa azumin yinin cikin sauki;

11 Kayi sallar Azahar, ka cigaba da kabbarori, azkar da karatun Alqur'ani.

12 Kayi sallar La'asar, Sannan ka cigaba da zikiri da karatun Alqur'ani har zuwa daf magriba
 (ga maza, mata kuma sai a tafi kitchen a je ana girki ana kabbarori).

13 Ka cigaba da addu'o'i daf da Kiran sallar magriba, ka roki ALLÃH Alkhairan duniya da lahira. Kada ka manta da 'yan uwan ka musulmai da kasar ka cikin addu'o'in ka. Ka tuna ranar da za ka tsaya gaban ubangijin ka. Ka roki ALLÃH kada rana ta fadi ba tare da an gafarta maka ba.

14 Ana kiran sallar magriba- ka sha ruwan azumin ka. Sannan kada ka manta kayi addu'a. Tafi kaje kayi sallar magriban ka. In shaa ALLÃH ka dace da Alkhairan ranar Arafah.

 *N.B* :
Mafi girman ibada a wannan rana itace azumi kamar yadda Annabi SAW ya ambata cewa azumin ranar Arafah yana kankare zunubban shekarar da ta gabata da kuma mai zuwa.

ALLÃH YA sa ni da Ku cikin wadannan wadanda za a 'yanta su daga wuta Sannan kuma ayyukan su za su zama kar6a66u.

Ka yada ma wasu suma su amfana za ka samu lada.

Share this


Author: verified_user

1 comment: