Labarai

Rashin Kunya Ne Mace Ta Fito Neman Miji A Kafofin Sada Zumunta ~ Datti Assalafy

Akwai wani sabon yayi da wasu fitsararrun ‘yan Mata suka fito dashi, suna daukar bidiyon kansu su sanya a kafofin sada zumunta wai suna neman mijin aure, sun gaji da zama a gidan iyayensu ya kamata wai azo a auresu

Wannan dabi’a ne ta yahudu da nasara wadanda ba su gaji mutunci da daraja  da kunya ba, kuma dabi’a ce ta karuwai da suke tallan kansu ko ake talle da su a biyasu kudade

Babu wani mutum mai daraja da zai kula irin wadannan mata masu tallan kansu a kafofin sada zumunta, don abinda zai zo ransa shine ta gama yawon iskancinta ne dare ya mata shine ta fito neman wanda zata cuceshi

Duk wani abu mai daraja killaceshi ake, kuma an san mace da kunya, rashin kunya ne tsantsa ki dauki bidiyo ki saka a media wai kina neman mijin aure, gaskiya babu wani mutumin kirki da zai kulaki sai tataccen ‘dan iska wanda zai zo don biyar bukatarsa ya gudu

Idan kina da matsala na rashin mijin aure ki kiyaye dokokin Allah ki dage da rokon Allah kina tashi da dare kiyi sallolin nafila babu shakka Allah Zai cika miki burinki, Ya kawo miki mijin kirki

Idan ya kama sai kin tallata kanki misali kina da wata lalura ke kharija ce, kina bukatar na miji mai karfin jima’i da zai gamsar dake a gurin saduwa, ko kina da matsala na Aljanu suna addabarki kina bukatar Ustazun gaskiya Mahaddacin Qur’ani da zai kula da ke wajen yin ruqya, da sauran matsaloli, to zaki iya bawa wasu bayin Allah kamar Limamin unguwa su nemo miki mijin da ya dace dake ta hanya mai kyau

Amma tallen kanku da kuke a media sam bai dace ba, wauta ne da rashin hankali da kuma batan basira da nuna mana cewa baku da tarbiyya da kunya, ku sani duk abinda kuka saka a media har jikoki da ‘ya’yanku sai sunzo sun gani, ya zakiji ace ‘danki watarana ya zo ya ga bidiyonki kina tallen kanki wajen neman mijin aure? ai baki kyautawa yaranki ba

Kuma kamar kuna nuna mana ba’a gaban iyayenku kuke ba, baku da mafadi da zai baku shawara, don babu wani uba da zai yarda ‘yarshi ta dauki bidiyon kanta tana jawabin neman miji ta sanya a kafofin sada zumunta, mai aikata wannan bata da mafadi, zaman kanta take ko kuma ballagaza ce  mai bakin iyaye

Don haka kuyi hankali, wannan ba mutunci bane, kuma ba wayewa bane

Allah Ya sa ku gyara

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button