Tuesday, 28 July 2020
Mun Bankado Shirin Da Ake Yi Wa Nijeriya Domin A Tarwatsata, Cewar DSS

Home Mun Bankado Shirin Da Ake Yi Wa Nijeriya Domin A Tarwatsata, Cewar DSS
Ku Tura A Social Media


Daga Muhammad Kwairi Waziri , walikin rariya

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS tace ta gano wani shiri da wasu manyan ƙasar nan da suke yi na ganin sun tarwatsa Nijeriya.

A cikin wata takarda da jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Peter Afunanya ya sanya wa hannu kuma aka rarraba ta ga manema labarai, ya ce sun gano shirin manyan ne na ƙoƙarin jefa gaba ta ƙabilanci da bambancin addini tsakanin jama’ar Nijeriya, domin cimma manufar su ta tarwatsa ƙasar baki daya.

Rundunar ta ƙara da cewar ‘yan sandan farin kaya da sauran ƙwararru na rundunar na iya bakin kokarin su domin ganin haƙar mutanen bata kai ga ruwa ba.

“Lallai bayanan sirri sun zo mana akan aniyar waɗannan mutane da waɗanda ke ɗaukar nauyin su akan aika-aikar ta su, kuma ko kaɗan hukumar mu ba zata lamunci duk wani shiri da zai haifar da rudani gami da kawo tashin hankali a Najeriya ba.

Sanarwar ta buƙaci jama’ar Nijeriya masu kishi da su taimaka wa hukumar tasu da bayanai na sirri da kai rahoton dukkanin wani gungun jama’ar da basu amince da su ba.

Share this


Author: verified_user

1 comment: