Friday, 31 July 2020
Labari Mai Dadi : Sako Mai Muhimmanci Gare Mu ~ Datti Assalafy

Home Labari Mai Dadi : Sako Mai Muhimmanci Gare Mu ~ Datti Assalafy
Ku Tura A Social Media


Babban kamfanin sadarwan dake Nigeria, mallakar kasar South Africa, wato kamfanin "Mobile Telephone Network" ko "MTN" a takaice, ya ware wasu kudade masu yawa domin gabatar da ayyukan raya kasa a unguwannin dake 'kauyuka da kar-kara da biranen Nigeria, MTN sun ce ayyukan zai kasance a cikin unguwanni ne

Yadda za kuyi ku samu MTN ta zabi unguwar ku shine: zaku shiga message a wayar ku, ku aika da sakon "MTN" zuwa ga 321, daga nan zasu aiko da sako na biyu a take, zasu ce ka saka cikakken sunan ka, ka sake aikawa  321, za suyi maka tambayoyi tare da bukatar ka shigar da sunan unguwar ku, da wurin da kake so ayi muku wannan aiki.

Dayan abubuwa uku ne MTN suka ce za suyi wa dukkan unguwannin da aka zabe su:
1-Solar Power? hasken wutar lantar mai amfani da hasken rana  kake so a saka wanda zai rika haska unguwar ku?
2- Aikin samar da ruwan Borehole tuka-tuka/burtsatse kake su ayi a unguwarku?
 3- Gina 'dakin kimiyyar computer a makarantar Sakandaren gwamnati dake unguwar ku?
Wato ICT Lab?

-Idan ka zabi wutar solar ne kake so su gina a unguwarku, sai ka aika da lamba 1 zuwa ga 321
-Idan ruwan borehole ne kake so suyi a unguwarku sai ka aika da 2 zuwa ga 321
-Idan kuma Computer Lab kake so su gina a unguwarku, sai ka aike da 3 zuwa ga 321.

Daga karshe zasu tambaye ka cewa ka sanya lambar wani mutumin unguwar ku wanda za'a iya tuntubar sa, sai ka saka lambar wani mai daraja a unguwar ku, wanda kake ganin yana da damuwa da irin wadannan abubuwan da al-umma ke bukata, musamman idan kana da lambar wani wanda zai iya magana da Turanci, wanda idan an kira shi zai tuna maganar da ka gaya masa, kuma yayi jawabin da ake bukata, ko mahaifin ka kana iya saka lambar sa.
Amma sai ka sanar dashi cewa koda yaji an kira ana tambaya to ya amsa yanda ya kamata.

Daga karshe zasu turo maka sako cewa zasu tuntubeka idan unguwar ku tayi nasarar shiga sahun wadanda za'a musu aikin.

Yadda za kuyi shine, matasan unguwar ku duk su cika su aike da sakon wa MTN kamar yadda bayani yazo a farko, ku saka abu iri daya, to ana kyautata zaton idan suka ga sako iri daya yayi yawa, da sunan unguwa 'daya, kuma bukatar iri daya ne, to zasu dubi unguwar ku.
Misali, mutane dari biyu a unguwar ku su aike da sakon suna bukatar ruwan borehole, ko solar ko ICT Lab.

Sannan duk sakon daka tura to kar ka sake aikawa da wani sakon sai sun turo maka tambaya ta gaba, sai ka amsa ka tura, sai ka sake jiran su, zasu aiko maka da tambaya ta gaba, cikin minti biyu ko uku zaka kammala wannan aikin.

Idan Allah Ya sa anyi nasara unguwar ta shiga, to kaima zaka samu ladan kokarin da kayi wurin kawo wannan alherin unguwar ku ko garin ku, kar muyi wasa da wannan shirin na MTN, a kullun Arewa ana barin mu a baya

Jama'a ku taimaka wajen yada wannan sakon

Allah Ya sa a dace Amin

Share this


Author: verified_user

1 comment: