Tuesday, 28 July 2020
El-Rufa'i ya rushe wata makaranta bisa samun mai ita da laifin fyade ( A Cikin Hotuna)

Home El-Rufa'i ya rushe wata makaranta bisa samun mai ita da laifin fyade ( A Cikin Hotuna)
Ku Tura A Social Media

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i, ya rushe makarantar Liberation Collage dake cikin garin Kaduna bayan an samu mai makarantar Mista Samuel Ejikeme da laifin yi wa yarinya 'yar shekara 9 fyade.

Wani dalilin da ya kara tunzura gwamnatin yin lubur da makarantar kamar yadda wani hadiminsa a fannin yada labarai Abdallah Yunus Abdallah ya bayyana, shine rashin samun sahalewar gwamnati kafin gina makarantar. Kazalika aka samu Mista Samuel na amfani da makarantar wurin lalata yaran mutane.


Dokin Karfe na ruwaito

Share this


Author: verified_user

1 comment: