Thursday, 30 July 2020
Bidiyo : Kamin Gwamna Zulum ya je Baga, Sojoji sun Bashi Tabbacin cewa Babu Boko Haram a Garin ! Kalli Irin Cacar Baki Tsakaninsa Da Sojoji

Home Bidiyo : Kamin Gwamna Zulum ya je Baga, Sojoji sun Bashi Tabbacin cewa Babu Boko Haram a Garin ! Kalli Irin Cacar Baki Tsakaninsa Da Sojoji
Ku Tura A Social Media
Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da harin da aka kaiwa gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum a jiya, Laraba a yayin da yake kan hanyar shiga Baga.

Me magana da yawunsa, Malam Isa Gusau ne ya tabbatar da haka ga BBChausa, yace kamin gwamnan yaje Baga, sojoji tun tuni sun bashi tabbacin cewa sun kwato garin Baga daga hannun Boko Haram.
Yace amma gwamnan ya bar Monguno yana kan hanyar zuwa Baga sai kawai suka fara jin harbin bindiga. Yace jami’an tsaron dake tare da gwamnan sun maida Martani inda wasu dake tawagar gwamnan suna bar wajan da rarrafe.

Yace gwamnan bai karasa garin na Baga ba, ya koma Monguno ya kwana.

Hakanan Hutudole ya samo daga shafin daya daga cikin hadiman gwamnan, Habu Kale Tijjani wanda ya bayyana hoton bidiyon da gwamnan ke caccakar sojojin da cewa babu alamar cewa suna aiki yanda ya kamaya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: