Wednesday, 1 July 2020
Ajimobi : Diyar Ganduje Ta Mayarwa Masu Sukar Surukinta Bayan Ya Mutu Martani Mai Zafi

Home Ajimobi : Diyar Ganduje Ta Mayarwa Masu Sukar Surukinta Bayan Ya Mutu Martani Mai Zafi
Ku Tura A Social Media
Fatima Ganduje-Ajimobi, ‘Diyar gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta sa baki a game da rikicin da ya ke nema ya kaure bayan mutuwar mahaifin mijinta.

A makon da ya gabata ne tsohon gwamnan jihar Oyo watau Sanata Abiola Ajimobi ya rasu. Hajiya Fatima Ganduje-Ajimobi ta na auren ‘dansa Idris Abiola Ajimobi.

Tun da Abiola Ajimobi ya cika ake samun sabani tsakanin gwamnan jihar Oyo ta PDP da iyali da magoya bayan tsohon gwamnan.

A ranar Talata, 30 ga watan Yuni, 2020, Segun Awosanya wanda aka fi sani da @Segalink ya fito Twitter ya na yabon gwamnatin Oyo kan matakin da ta dauka bayan rasuwar Ajimobi.

Awosanya ya rubuta: “Ban san adadin mutanen da su ka yi murna da yadda Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo ya ki biyewa tarkon da ake nema a yi wa mutanen jihar Oyo ba.”

“Ni na ji dadi da ya gane manakisar da aka shirya” - @Segalink.

Mista Awosanya ya yi wannan magana ne a ranar Litinin da kimanin karfe 12:43. Washegari da yamma, sai Fatima Ganduje-Ajimobi ta maida masa martani ta shafinta na Twitter.
A cewar Ganduje, Abiola Ajimobi ya sha gaban Injiniya Seyi Makinde, kuma gwamnan mai-ci, ba zai iya sa kafa a inda Marigayin ya taka ba.

‘Diyar gwamnan na Kano ta yi dariya ta ce: “Jirwaye ya na da hadari. SM (Seyi Makinde) ba zai taba zuwa ko da kusa da Ajimobi ba, har abada.”

Surukar tsohon gwamnan ta kara da cewa: “Ba sa’an ku ba ne!!!”

Wasu sun fito su na sukar Ganduje kan tsoma baki cikin siyasar jihar Oyo da ba ta da ilmi a kai.

Wannan ne kusan karon farko da Fatima Ganduje-Ajimobi ta yi magana a Twitter, bayan ta fito ta karyata rade-radin da aka rika yi na mutuwar Ajimobi a lokacin da ya ke kwance a asibiti.

A makon jiya Bazawar marigayin ta samu kanta ta na cacar baki da mataimakin gwamnan jihar Oyo. Florence Ajimobi ta ce gwamnatin PDP ta sa siyasa a lamarin mutuwar mai gidanta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: