Kannywood

Yan Kannywood suna taya Ganduje yaƙi da cutar korona


Taurarin fina-finan Kannywood sun bi sahun gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya wajen yaki da cutar korona.
Taurarin sun dukufa wajen wayar da kan jama’a kan illar cutar da kuma matakan da jama’a za su bi wurin kauce wa kamuwa da ita, kamar yadda Ma’aikatar Lafiyar jihar ta bayyana a shafinta na Twitter ranar Lahadi.
An ga fuskokin taurari irin su Yakubu Mohammed, Saratu Gidado (Daso) Aminu Shariff (Momo), Rukayya Dawayya, Dan Azumi Baba Chediyar, Abba Al-Mustapha da makamantansu a taron wayar da kan jama’a da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta hada ranar Asabar.
Ya zuwa ranar Asabar da almuru, mutum 1,195 aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Kano ko da yake an sallami mutum 835 bayan sun warke, amma ta kashe mutum 51.
A kwanakin baya, Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a saba gani ba a jihar.
Sai dai gwamnatin Kano ta musanta rahoton tana mai cewa: “Mutum 255 cikin 1604 da suka mutu, wato kashi 15.9… ne suka mutu sanadin cutar korona. Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci saboda fargabar annobar korona.”

Social embed from twitter

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *Back to top button