Tuesday, 30 June 2020
Wannan shine Cin Amanar ! Talaka Da Wasu 'Yan Majalisar Tarayya Suke Yunkuri Yiwa Talakawan Nigeria Akan Daukar Matasa Aiki 774,000

Home Wannan shine Cin Amanar ! Talaka Da Wasu 'Yan Majalisar Tarayya Suke Yunkuri Yiwa Talakawan Nigeria Akan Daukar Matasa Aiki 774,000
Ku Tura A Social Media


Tsarin da shugaba Buhari ya kawo zai dauki  mutane dubu dari bakwai da saba'in da hudu aiki wanda a kowace karamar hukuma za'a dauki mutum dubu daya

Amma abin takaici sai ga wasu 'yan majalisar tarayyya suna yunkurin kawo tarnaki, suna so su karbe ragamar daukar aikin, ta yanda wato sai 'yan jagaliyar siyasarsu kawai zasu samu

To amma Alhamdulillah Ministan kwadago Barr Festus Keyamo ya mayar da raddi wa 'yan majalisar, yace:
" 'Yan majalisar 'kasa basu isa su bamu umarni akan wannan aikin ba, bayan shugaban Kasa yace mu je mu dauki ma'aikata dubu 774,000 babu wanda ya isa ya tsayar damu, Buhari ne kawai zai iya dakatar da wannan aikin".

Hakika 'yan majalisar da sukayi yunkurin kawo tarnaki akan wannan abin sunyi abin kunya da Allah wadai, sunyi abin kunya saboda sun guji al'ummarsu, sai yanzu da shugaba Buhari ya kawo tsari mai kyau suke so su karkatar, Insha Allahu burinsu ba zai cika ba

Allah Ka taimaki shugaba Buhari Ka raba tsakaninsa da maciya amana Amin

Daga Datti Assalafy

Share this


Author: verified_user

0 Comments: