Kannywood

Waƙar Da Na Yi wa Jonathan Ta jefa Ni cikin Ruɗani – Nazifi Asnanic

Shahararren mawakin Hausa Nazifi Asnanic ya shaida wa BBC cewa a tarihin wakokinsa ba zai taba mantawa da wakar da ya yi wa tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ba.
Kodayake mawakin ya ce ya fi kaunar wakar da ya yi tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta ‘Dawo-Dawo’, amma wadda ya yi wa Jonathan ta tsaya matsa a rai saboda yanayin da ya shiga.
Mawakin ya bayyana hakan ne lokacin wata hira da muka yi da shi kai-tsaye a shafinmu na Instagram.
Ya ce bayan ya riga ya yi wa Jonathan waka ta yi karfi, sai ga shi kuma a shekarar 2015 yana so ya kara tsayawa takara “lokacin kuma masu son Buhari sun taru sun yi yawa.”
Asnanic ya ce a lokacin ya shiga rudani saboda wakar Jonathan ta ƙi bacewa, “ga shi kuma muna son mu yi tallan Buhari. Wannan ya sa ba zan iya mantawa da wakar ba,” in ji shi.
“Amma ni ban yi da-na-sanin yin wakar ba saboda ai a lokacin da na yi Jonathan ne ke mulki. Ina son wakar kuma ina son yadda na rubuta wakar.”
Hakazalika shahararren mawakin ya ce wakar da yi wa Kwankwaso ba za ta taba bace masa a rai ba.
Ya ce yana jin dadin ta kuma yana alfahari da wannan ita. “Duk kasar da na je kafin a fada min wata waka, ita ake fara fada min.”

Wane ne Nazifi Asnanic?

AsnanicHakkin mallakar hotoALOMAR PHOTOGRAPHY
Image captionAsnanic yana da mata Fatima da kuma ‘ya’ya uku
Asnanic ya ce an haifi shi kimamin shekara 33 da suka wuce a unguwar Durumin Iya a jihar Kano, inda a nan ne ya fara karatun allo da na boko.
Ya ce cikakken sunansa Nazifi Abdussalam Yusuf, amma “Asnanic” ya samo shi ne a makaranta, inda ya dauko wasu bakake daga sunan mahaifinsa da sunan wata abokiyar aikinsa da sunan wata karamar yarinya mai kaunar wakarsa daga nan ne ya tayar da kalmar Asananic.
Mawakin ya ce ya fara waka ne don shi ma ya bayar da gudunmuwarsa wajen ci gaban al’umma, amma ya ce ya kwashe lokaci mai tsawo yana rubuta waka kafin shi da kansa ya fara rera ta.
Daga nan mawakin ya yi karin haske kan abin da ya sa ba ya fitowa a fina-finan kamar wasu takwarorinsa mawaka, inda ya ce shi ba ya sha’awar fitowa ne kuma “gaskiya ma ni ina tsoron kyamara ne,” a cewarsa.
“Ni na fi so na ci gaba da zama a bayan kyamara, amma daga bayan nan na rage jin tsoron ta,” in ji shi.
Har ila yau Asnanic ya ce sabanin yadda wasu mawaka suke shan wuya wajen samun karin waka yayin shirya ta, ya ce shi rubuta waka ne ya fi ba shi wahala.
NAZAFI ASNANICHakkin mallakar hotoNAZIFI ASNANIC/INSTAGRAM
Image captionSami Yusuf da Ommou Sangari ne mawakan da suka fi burge shi a duk duniya
Shahararren mawakin ya ce akwai wata lambar yabo da aka taba ba shi a Jami’ar Bayero ta Kano wadda ba zai taba mantawa da ita ba.
Ya ce a bangaren wakokin fina-finan Hausa da kuma soyayya ya fi son wakar da ya yi a fim din Fil Azal ta Soyayya In Za Ka So Dan uwanka…
Hakazalika ya ce babban burinsa shi ne ya ga yana tallafawa na kasa da shi.
Sami Yusuf da Ommou Sangari ne mawakan da suka fi burge shi a duk duniya.
Asnanic ya ce yana da mata Fatima da kuma ‘ya’ya uku.
Wacce jam’iyya yake goyon baya?
Asnanic ya ce babu shakka kowa ya san shi tare da Sanata Kwankwaso na jam’iyyar PDP, amma a kwanakin baya sai aka gan shi yana tallan Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.
Ya ce wannan ya sa aka kasa gane wacce jam’iyya yake goyon baya tsakanin manyan jam’iyyun Najeriya biyu.
“Na yi hakan ne saboda lokacin Sanata Kwankwaso ba zai takarar shugabancin Najeriya ba, shi ya sa na dauko tallan Buhari a sama, a Kano kuma muna tallan PDP,” in ji mawakin.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button