Uncategorized

Maganar Wasa ta zama Gaske, Har An kai ga Daura Aure a Yau Asabar

Maganar Aure kamar da Wasa, ta Tabbata Gaskiya Tsakanin Masoya a Kontagora Jihar Neja

Da misalin ƙarfe biyu na yau asabar 13 ga watan July 2020 aka ɗaura auren Jamilu da Nasiba waɗanda suka fara zancen auran nasu a ranar litinin 9 ga watan July 2020 kamar da wasa a garin Kontagora ta Jihar Neja.

labarin da kafafen sadarwa suka wallafa tare da gabatar da shirye shirye a gidajen radio daban daban akan auran wanda yaja hankalin duniya inda al’umma dadama suka ta bayyana ra’ayoyin su mabanbanta dangane da al’amarin.

An ɗaura auren ne a garin Libele dake ƙaramar hukumar Magama a Jihar Neja biyo bayan sadakin naira dubu ashirin lakadan da ango ya biya, inda aka gabatar da sigar aure kamar yadda addinin musulunci ya tanadar malammai kuma sukayi addu’o’i da fatan alheri akan auran.

Ɗaurin auran ya samu halartar ɗinbin al’umma daga kusurwa daban daban waɗanda suka halarci garin domin shaida ɗaurin auran dake cike da abun mamaki da farin ciki. Jimkaɗan bayan kammala ɗaurin auren wakilin mu ya samu zantawa da angon mai suna Jamilu Yusuf inda ya bayyana matuƙar farin cikin sa tare da godiya ga ƴan uwa da abokan arziki da ɗaukacin al’umma na irin gudunmuwa da addu’o’in fatan alheri da suka riƙayi mai dangane da auran nasa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button