Kannywood

Hamisu Breaker: Farfesa Gusau ya feɗe waƙar Jarumar Mata

Waƙar Jarumar Mata da ta ja hankali a arewacin Najeriya yanzu kuma ta samu shiga fagen nazari a Jami’a, inda mashahurin malamin nazarin adabin baka Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya feɗe waƙar.

Kwarjini da karɓuwa da kuma daɗin waƙar da salonta ake ganin ya ja hankalin masoya musamman matan aure da aka gani a bidiyo suna rausawa a gaban mazajensu, a daidai lokacin da ake cikin yanayin zaman gida na kullen annobar korona.
Ana nazarin waƙa ne a fagen ilimi idan ta dace da nazari da kuma abubuwan da nazari yake nema, ƙila wannan ne dalilin da ya ja hankalin Farfesa Gusau mashahurin malamin waƙoƙin baka a Jami’ar Bayero da ke Kano.
Farfesan ya feɗe waƙar ne a wata takardar nazari da ya aiko wa BBC mai taken “Feɗe waƙar Jarumar mata ta mawaki Hamisu Yusuf Breaker bisa gadon nazarin waƙar baka Bahaushiya.”
Hamisu Breaker ya saki waƙar Jarumar Mata ne dab da bikin Sallah ƙarama, kuma sai ga shi ta samu ƙarɓuwa nan da nan inda wasu matan aure suka ci bikin na sallah da waƙar tare da ɗebe kewar zaman gida.
A wata hirarsa da BBC, Hamisu Breaker ya ce yakan yi waƙa ne da za ta shafi samari da masu manyan shekaru, sai gashi ta ƙarɓu ta ƙara masa farin jini kuma har ta shiga fagen manyan masu nazarin adabin baka.

Ga yadda Farfesa Gusau ya feɗe waƙar

Waƙar Jarumar Mata tana da yawan ɗiya aƙalla guda goma sha biyar (15). Waƙar ta zama ruwan dare game duniya a tsakanin mutane tun ma ba Hausawa ba.
Hamisu Breaker ya yi wannan waƙa ne da harshen Hausa bisa kari na Kananci. Domin haka, mutane tun ma ba matasa ba sun yi hidimar haddace ta, tare da sassauya ta gwargwadon ƙauna da bukatar kowannensu.
Wata matar aure ce da ta ke nuna son mijinta, wani don son kuɗi wani don ƙaunar dabbobi kamar akuya, wani don buƙatar ya samu gida ko mota da sauransu.
Ta haka suke hawan waƙar, suna juya ta, ta amfani da kalmominsu amma bisa amo da yanayin rerawarta da kuma raujinta.

Short presentational grey line

Tarihin Mawaki

Sunan yanka na wannan makaɗi shi ne Muhammadu Hamisu, mahaifinsa kuma shi ne Sa’idu, sannan kakansa shi ne Yusufu. Unguwar Hamisu Breaker ita ce Ɗorayi Ƙarama a sashen Unguwar Bello, a Ƙaramar Hukumar Gwale, Jihar Kano.
An haifi Hamisu a shekarar 1992. Ya yi makarantar Firamare ta Gwamnati a Ɗorayi Ƙarama, ya kuma yi makarantar sakandare ta Gwamnati, ƙarama da babba duka a Ɗorayi Babba a Jihar Kano.
Haka kuma shi mutum ne mai riƙe abubuwa, mai kaifin hadda, mai mayar da maganganu kamar yadda ya ji su.
Hamisu Breaker ya fara waka ne a sa’ilin da yake a Makarantar ƙaramar Sakandare ta Dorayi Babba, a Jihar Kano, kuma har yau yana a kai. Allah ya ƙara masa basira da ɗaukaka.
Duk da yake Hamisu Breaker ya tashi da shirya waƙoƙi tun yana a makarantar allo, musamman waɗanda ya yi a tsakanin ƴan’uwansa ƴan makaranta na wasu Qasidu, amma ƴan shekaru kaɗan ya zama mawaƙi ko makaɗi kuma ya fara fitar da album nasa na farko a ƙarshen shekara ta 2016.
Lokacin ne ya fitar da album mai ɗauke da waƙoƙi aƙalla guda shida, yawancinsu kuma na soyayya ne.
Hamisu Breaker makaɗi ne wanda Allah ya ba mutane da yawa. Mawaɗi ne wanda ya yi shuhura a harkokin sadarwa na zamantakewar jama’a.
A Youtube kaɗai yana da mabiya fiye da dubu arba’in (40,000) ga kuma Facebook da Instagram da makamantansu.

Short presentational grey line

2.0 Saƙo ko Tarken Waƙar
2.1 Gundarin Turke
Babban saƙon da wannan waƙa ta ke ƙunshe da shi, shi ne nuna tsantsar soyayya irin wadda ta ke wanzuwa tsakanin masoyi da masoyiyarsa, wadda kuma bisa yawanci takan zama mutu ka raba ne.
Soyayyar masoyi zuwa ga masoyiyarsa ya ratsa wannan waƙa tun daga ɗanta na farko har kuwa zuwa ƙarewarta a ɗa na 15.
Wannan waƙa tana ɗauke da kalmomi masu fizgar zuciya, kuma masu sakaya zance bisa hikima da adonta masoyiya.
Kuma waɗannan kalmomi da aka zaɓo masu bayyana soyayyar masoyi ga masoyiyarsa ne waɗanda suke tafiya tamkar sautin jirgin ƙasa a yayin da ya darkako hanya.

Short presentational grey line

2.2 Muhallan Turke na waƙar:
A wasu misalai na muhallan turke na wannan waƙa su ne inda ɗa na 4 da ɗa na 5 suke faɗin:
Jagora: Tilas ganin mu tilas barinmu,
: Ƙaunarki tun da nai nisa,
: Sam ba batun na fasa ko za a ce mun in ba da rai fansa.
Jagora: Tsarin zubin ki daidai ne,
: Ya kama zuciyata ne,
: Ina ji kamar mafarki ne,
: Ina son ki so mataki ne.
(Breaker, Waqar Jarumar Mata, ɗa na 4-5)
Akwai kuma wani misali inda yake cewa a ɗa na 6
Jagora: Ni ban da damuwa in har zan buɗe ƴan idanuna,
: In kalle ki ga ki dab da ni,
: To me za ya dami ƙalbina.
(Breaker, Waƙar Jarumar Mata, ɗa na 6)

Short presentational grey line

2.3 Taƙaita Turke Waƙar
Sakonnin da wannan waƙa ta ƙunsa a gunduwa-gunduwa ta ma’ana sun haɗa da:
Ɗa na 1-2: Suna nuna ƙarfin son masoyi ga masoyiyarsa domin ko ana ha maza ha mata sai ya sami masoyiyarsa kuma daga nan ba zai sake tanka wa kowa ba. Wato buri ya cika.
Ɗa na 3: Masoyi ba zai kula kowa ba sai kawai masoyiyarsa
Ɗa na 4-5: Waɗannan ɗiya sun shafi muhallin tarke a inda masoyi ya yi ta kwatanta masoyiyarsa. A nan ne kuma masoyi ya nuna ba zai daina nuna soyayyarsa ga masoyiyarsa ba ko da ko zai mutu ne.
Ɗa na 6: Shi ma wannan ɗa wani muhallin turke ne a inda shi masoyi yake sauwara yana tare da masoyiyarsa. Domin haka babu wani abu da zai dami zuciyarsa ko ya ɗauke masa hankali.
Ɗa na 7-10: Suna nuna masoyi ya fahimci masoyiyarsa mai ɗaunarsa ce, mai cika masa muradinsa, mai kuma ceto nasa bisa kowane hali na rayuwa.
Ɗa na 11: Duk da ƙarfin son da wannan masoyiya ta ke nunawa, masoyin yana ganin a duniyar nan ba wanda zai iya ɗaukar tunaninsa sai kawai ita masoyiyarsa.
Ɗa na 12: Masoyi yana ba da shawara a kan soyayya ga duk wanda ya sarƙu da ita sai ya yi hanƙuri, musamman dangane da sauye-sauyen halayenta.
Ɗa na 14: Ɗan waƙar yana gargaɗin samari da ƴan mata a kan su dinga tafiya a sese a soyayya, kuma su yi hakuri da ita, sannan a daina gaugawa.
Ɗa na 15: Wannan ɗa na 15 shi ne wanda ya rufe wannan waƙar. Ɗa ne da yake yin faɗakarwa a kan masoyi yana taka tasa sa’a, haka kuma shi ma yana da rana ta shanya garinsa.

Short presentational grey line

3.0 Awon Baka na wannan waƙa
Yawan layuka na ɗa
Zubin ɗiya a waƙar – An buɗe waƙar ne da yanayin kiɗa na gangunan Turawa, sannan aka ci gaba kai tsaye da zuba ɗiyan waqar.
Tsarin ɗa ko ɗiya a waƙar
Tsarin Rerawa
Takidi a ɗiyan waƙar
Karin murya da amsa amon waqar

Short presentational grey line

4.0 Adonta Harshe a Waƙar
Alamtarwa = Kalmar Masoyi (ɗa na 15)
Kamantawa = ɗa na 5, da ɗa na 12, da ɗa na 13.
Siffantawa = ɗa na 2, da ɗa na 10.

Short presentational grey line

5.0 Aiwatar da harshen Waƙa
Yawan Kalmomi = 372 Kalmomi
Zaɓen Kalmomi = Misali rai, zuciyata, ruwa, iska, kewa, jure, jira, ɗau fansa, jimirin jiranki, sirrin rayuwa, gani, bari, maqiya kalamaina, da sauransu. Maganganun Hikima
Karin Magana: gani nan bari nan: ɗa na 4.
Wanda ya mutu ba ya jin kira: ɗa na 3.
Karin Harshe na Waƙar = Kananci
Ginin Jumla a Waƙar = Akwai nau’o’i daban-dabam, kamar:
Jumla Sassauƙa: ɗa na 6, ɗa na 14.
Jumla Tsattsaura: da na 2, ɗa na 12.
Jumla Korau: ɗa na 1, ɗa na 4.
Jumla Ƙanga Dogarau: ɗa na 11, ɗa na 8, ɗa na 10.
Jumlar Aikatau: ɗa na 8, ɗa na 10.
Yankunan Jumla: ɗa na 4, ɗa na 5, ɗa na 10.

Short presentational grey line

6.0 Tasirin Waƙar ga Al’ummar Hausawa
Waƙar jarumar Mata ta yi tashe sosai musamman ma a wajen matasa Hausawa, maza da mata, ma’aurata da marasa aure. Waƙar ta shiga zukatan matasa Hausawa ka’in-da-na’in, musamman a lokacin bikin Sallah ƙarama ta wannan shekara ta Lahadi 24/5/2020 Miladiyya.
Waɗannan matasa sun haddace waƙr, sun kuma yi maming nata dangane da soyayya da ƙauna da son rai daban-daban da suke nunawa.
Ina iya tunawa a tarƙe ko a nazarin waƙar baka akwai abubuwa biyu da za a yi la’akari da su a kowace waƙa da za a yi nazari kuma a ƙarfafa wa mutane su saurare ta.
Akwai waƙar da za a yi wa nazari wadda ta dace da al’adu kyawawa na al’ummar Hausawa kuma ta bi sharuɗɗa da dokokin addinin Musulunci da Hausawa suka yi imani da
shi kuma suke biya.
Sannan akwai waƙa Ballagazazziyar waƙa wato ita ce wadda ta saɓa wa al’adun al’ummar Hausawa da addininsu. Su kansu kuma zukatan masu sauraron wakoƙin baka kashi biyu ne.
Akwai zukata masu kyau waɗanda suke bin kyawawan dokokin al’adu da ƙa’idojin addinin al’ummarsu. Akwai kuma wasu zukatan waɗanda babu ruwansu da dacewar al’adu bisa godabu managarta ko kuma
abubuwan da addininsu suka zo musu da su na shiriya.
Har wa yau kuma wannan ya zama wani nuni ne na abin da zukata suke so kuma ko suke sha’awa.
A ma’ana ta lugga an bayyana Kalmar Zuciya da (i) ‘wata curarriyar tsoka da ta ke cikin ƙirjin mutum ko dabba ko tsuntsu wadda ke aika jini zuwa sauran sassan jiki. (ii) Fusata ko saurin fushi.
(iii) Sa zuciya, watau zaton aukuwar abin kirki. (iv) Qarfin Zuciya, watau jarunta. (v) Zuciyar maraya, watau wata irin saƙa mai fari da baqi. (vi) ya hau dokin zuciya, watau ya fusata. (vii) ajiyar zuciya,
watau numfasawa. (viii) ƙawa-zuciya, watau tsananin son abu. (ix) wadatar zuci, watau dangana’ (CNHN, Qamusun Hausa na Jami’ar Bayero: sh 495).

Short presentational grey line

Dangane da ma’anar zuciya ta fannin ilimin addinin Musulunci kuwa ita ce yadda Annabin Allah, sallallahu alaihi wa
sallama, ya ambata a cikin Hadisinsa na shida na littafin Al-Arba’una al-Nawawiyya yana cewa: Tabbas akwai wata tsoka a jikin ɗan’adam, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta ɓaci dukkan jiki ya
ɓaci. Lallai ita ce: Zuciya. Buhari da Muslim suka ruwaito shi (Qaura, Salihu Abubakar, 2017: 38-40).
Haka ne kamar yadda ya gabata, an sami matasa a wasu sassa na ƙasar Hausa, maza da mata, waɗanda suka shisshirya bidiyo, suna hawan waƙar suna rera wa , wasu mata ne waɗanda suke caɓa rawa a gaban mazajensu.
Wasu sun sanya abubuwan ƙaunarsu a gabansu suna bin wannan waƙa, suna kuma sassaka nasu ƙare-ƙare gare ta da sauran makamantan waɗannan abubuwa.
Wannan wani nau’i ne na rage zafin zaman gida, wataƙila ko ba komi sai don su kashe kwarkwatan zaman kulle na gida da aka saka su domin cutar korona.
Bisa al’adu na Hausawa da na addinin Musulunci da suka samu daga bisani, Hausawa dukkansu, maza da mata, an san su da jin kunya da sirranta abubuwa, tun ma ba mata nasu ba.
Namiji yake cewa mace yana son ta da aure amman ba ita macen ba. Zai yi wuya mace ta dubi idanun namiji, ta yi ido arba da shi, kuma ta gaya masa tana son sa ko tana ƙaunar sa ko tana begen sa.
Amma a yau, an sami tasire-tasire na zamani da haɗuwar Hausawa da wasu baƙin al’adu na jinsunan mutane daban-daban tun ma ba Turawa ba, sai wasu Hausawan suka kwaikwayi wasu baƙin al’adu har suka ƙanƙame su, suka dinga aiki da su.
Yau ga shi an cim ma wani lokaci matan aure na Hausawa wai su ne suke yi wa mazajensu waƙa, suna nuna soyayyarsu gare su, ba su bari mazajen su gaya musu waɗannan kalamai ba.
Wannan abun da ya faru ya haddasa ka-ce-na-ce da ƙalubale a tsakanin wasu Hausawa, musamman ma Malamai waɗanda suke ganin wannan wata hanya ce ta cin zarafin addinin Musulunci da koin-kula da shi. Wadannan Malamai suna ganin ba a nuna:
Tsoron Allah ba, da Kunya da Kishin iyali da ba ƙauna ce ba, ba mawadda ce ba domin ba a nuna sirri ba, kamar yadda al’adun Hausawa suka amince.
Kuma addinin Musulunci ya yarda a dinga sirrintawa a kan aiwatar da abubuwa. Dubi misali a Alƙur’ani, mai girma Suratu al-A’araf, aya ta 33.

Short presentational grey line

Sannan kuma akwai maganar Halifa Sayyadina Umar ibn Haɗɗabi inda ya yi wa wani mutum wanda yake magana da matasa a ƙofar gidansa kandarko har ya zungure shi da sanda yana faɗin: “A fa qofar
gida kake”. Shi ko mutumen ya gaya masa, “ai yana bisa dokin ƙofar gidansa ne, kuma yana magana ne da matarsa.”
Sai Sayyadina Umar ya nuna masa, ‘Ashe babu sirri a magana, kowa yana jin ka, yana kuma ganin ka, kuma Allah ya umurci a yi sirri a tsakanin iyali’.
Amma idan aka dubi wannan waƙa ta Jarumar Mata da nutsuwa, za a ga haƙiƙa ta dace da a yi nazarinta kuma a iya sauraronta, kuma mai nazari ya yi bugun gaba da ita.
Waka ce wadda ba ta saɓa ƙa’idojin fiɗar waƙa ba, kuma ba ta taɓa al’adun al’ummar Hausawa ko dokokin addininsu na Musulunci ba.
Wasu mutane ne suka ɗauke ta suka jujjuyata ta yadda zukatansu da sha’awace-sha’awacensu suke so.
Kuma su masu son waɗannan al’adu waɗanda za a iya kira munana ne, sun yi gamon katar da wannan waƙa ta Jarumar Mata, makaɗin ya sake ta ko ya fitar da ita.
Daga nan suka ɗauke ta suka dinga jujjuya ta, ta yadda suke bukata, kowane rukuni bisa gwargwadon abin da zuciyarsa ta ke ƙauna, kamar dai yadda aka bayyana a baya.
Hasali ma dai waƙar tana qarfafa soyayya da mawadda a tsakanin mutane. Ta haka ne Kamilu Dahiru Gwammaja yake tofa albarkacin bakinsa a kan waƙar yake faɗar:
‘Waƙa ce mai taɓa zuciya, mai sakaya zance kuma ta ƙunshi wasu maganganu na hikima, ga ta mai adonta harshe (Ganawa da Gwammaja, K.X., ranar Talata 9/6/2020 da qarfe 9:30 na dare).
Domin haka, a fahimta ta, wannan waƙa ta Jarumar Mata ta cancanci nazari.
Farfesa Saidu Muhammad GusauSashen Nazarin Harsunnan Najeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

One Comment

 • Leave a Reply

  Your email address will not be published. Required fields are marked *

  Back to top button


  WeCreativez WhatsApp Support
  Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
  👋 Hi, how can I help?