Saturday, 27 June 2020
DA ZINAR WURI GWANDA AUREN WURI ! Kalli Hotunan Ango Da Amaryarsa Kafin Aure

Home DA ZINAR WURI GWANDA AUREN WURI ! Kalli Hotunan Ango Da Amaryarsa Kafin Aure
Ku Tura A Social Media

Tun jiya nake ganin wannan hoton yana yawo, mutane suna tofa albarkacin bakinsu tsakanin 'yan boko aqeedah da musulmin kwarai

Tambayoyi sunzo a raina:
-Wannan 'yar sa ce?
-Wannan kanwarsa ce?
-Wannan 'yar uwarsa ce na dangi?
-Wannan shirin film ne?
-Wannan matarsa ce da zai aura?
Hankalin mutane yafi karkata ga cewa matarsa ce da zai aura

A zahiri wannan yarinya bata balaga ba, amma duk da haka za'a iya daura mata aure, Sheikh Aminu Daurawa ya taba bada fatawar cewa za'a iya aurar da 'ya mace tun tana jaririya, sai dai ba za'a kaita gidan miji ba har sai ta girma ta balaga

Balagar 'ya mace ya danganta ga yanayin girmanta, da jin dadin rayuwarta, da yanayin gurin da take rayuwa, balaga ba yana ga shekaru bane, shekaru 18 da ake batu shine karshen matakin shekaru da kowani mutum zai kai wanda ya zama cikakken balagagge

Don haka wannan ba abin tayar da jijiyan wuya bane, Musulunci abune mai sauki, da zinar wuri gwanda auren wuri, 'yan uwa da zaran yaranku mata sun balaga kuma suna son aure to ku aurar da su kafin gayu su lalata su

Yaa Allah Ka sanya albarka a rayuwar mu.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: