Tuesday, 30 June 2020
Da duminsa: Gwamnatin tarayya Ta Rage kudin Aure a Najeriya

Home Da duminsa: Gwamnatin tarayya Ta Rage kudin Aure a Najeriya
Ku Tura A Social Media
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta rage kudin gudanar da aure a Najeriya. Sabon kudin da ta sanya zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuli.

Sabon kudin ya zo karkashin dokar aure ta CAP M6 LFN 2004, a cewar sanarwar da babban sakatare kuma mai rijistar aure a Najeriya, Georgina Ehuriah.

Wata sanarwa daga daraktan yada labarai na ma’aikatar cikin gida ta Najeriya, Mohammed Manga, ta bayyana cewa hakan wani garambawul ne da gwamnati za tayi a fannin auren bayan samun shawarwari daga masu ruwa da tsaki a kwanan nan.

Lasisin yin aure a wuraren bauta an rage shi daga N30,000 na tsawon shekara biyu zuwa N6,000 a kowacce shekara.

Sabunta lasisin auren a wajen bauta, an amince a dinga biyan N5,000 a kowacce na tsawon shekara uku. Yayin da a da yake N30,000 kowacce shekara.

Hakanan an rage kudin daurin aure daga N21,000 zuwa N15,000, inda aka rage kudin lasisi na musamman daga N35,000 zuwa N25,000.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: