Sunday, 28 June 2020
Albishirinku Matasan Nigeria Wadanda Basu Da Aikin Yi Za'a Dauki Matsa Dubu Dari Bakwai Da Saba'in 774,000

Home Albishirinku Matasan Nigeria Wadanda Basu Da Aikin Yi Za'a Dauki Matsa Dubu Dari Bakwai Da Saba'in 774,000
Ku Tura A Social MediaIdan Allah Ya kaimu gobe Litinin, Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya zai rantsar da kwamitin da za suyi aikin 'diban matasa dubu dari bakwai da saba'in da hudu (774,000) a jihohin Nigeria 36 har da Abuja

Tsarin diban aikin zai kasance mutane dubu daya (1000) daga kowace karamar hukuma a Nigeria, wadanda zasu su dinga karban Naira dubu ashirin (20,000) duk wata a tsawon lokaci da aka tsara za suyi aikin, shirin zai fara aiki nan da watanni biyu masu zuwa, farkon watan October Insha Allah

Idan an kafa kwamitocin gobe; zasu isa jihohin su domin kafa kwamitocin kananan hukumomi, daga bisani za'a sanar da tsarin aikin da yadda mutane zasu shiga, wannan abin alheri yana zuwa ne a zangon karshe na mulkin shugaba Buhari wanda yake fatan ya rage wa matasa maza da mata radadin rashin aikinyi, kuma wannan sabon tsarin daban ne bayan N-POWER

Shugaba Buhari alheri ne, bai cancani ayi masa tawaye ba balle zanga-zanga, 'yan uwa matasa mu taimaka masa da addu'ah da kuma hakuri domin ya share mana hawaye

Yaa Allah Ka taimaki shugaba Buhari, Allah Ka raba tsakaninsa da maciya amana, Allah ka fitar dashi kunyar duniya da na lahira Amin

Share this


Author: verified_user

0 Comments: