Labarai

Akwai Yiwuwar Gwamnonin Apc Biyar Da Suka Hada Da El-Rufai, Abubakar Badaru, kayode , Bagudu,Simon Lalong Su Fito Takarar Shugaban Kasa A 2023

Akwai Yiwuwar Gwamnonin APC Biyar Da Suka Hada Da Atiku Bagudu Na Kebbi, Nasir El-Rufai Na Kaduna, Abubakar Badaru Na Jigawa, Kayode Fayemi Na Ekiti Da Simon Lalong Na Jihar Filato Su Fito Takarar Shugaban Kasa A 2023

Daga Comr Abba Sani Pantami

Wani daga cikin jagororin jam’iyyar hamayya a kudancin Najeriya, Prince Kassim Afegbua, ya sa baki a rigimar cikin gidan da ake yi a APC, wanda har ya kai aka sauke shugabanni na kasa.

Mista Prince Kassim Afegbua ya na ganin cewa an sauke Adams Oshiomhole da majalisarsa ne saboda harin siyasar 2023 inda za a samu sababbin zubin ‘yan takarar shugaban kasa a APC.

Kassim Afegbua ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi wata hira da jaridar Vanguard a jiya.

Babu wani abin a zo – a gani game da sallamar Adams Oshiomhole daga jam’iyya. Lissafin 2023 ce ta sa ya rasa kujerarsa, musamman ga wadanda su ke ganin zai yi masu taurin juyawa.” Inji sa.

Tsohon kwamishinan na jihar Edo, Afegbua ya zargi wasu gwamnonin APC da wannan aiki.

Shugaban kasa bai iya fahimtar siyasar da aka bugawa ba. Ka na da gwamoni irinsu Atiku Bagudu na Kebbi, Nasir El-Rufai na Kaduna, Abubakar Badaru na Jigawa, Kayode Fayemi na Ekiti da Simon Lalong na jihar Filato wadanda ya kamata su tsaya su yi aiki, amma su na hangen takarar 2023.” Inji Kassim Afegbua.

A cewar Prince Kassim Afegbua, wadannan gwamnoni biyar da su ke wa’adin karshe su na da burin fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin jam’yyar APC mai mulki.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button