Labarai

Abu Yayi Zafi !! A cire Kayan Aikin Masu Yin Fyade ~ Gwamna Nasir El-Rufai

A Yanke Hukuncin Dandaka Ga Duk Wanda Aka Kama Da Laifin Fyade, Cewar Gwamna Elrufai

Daga Ibrahim Dau Mutuwa Dole

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i, ya ce babbar hanyar magance matsalar fyade ita ce yi wa masu aikata laifin dandaƙa.

Malam Nasir ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar ta bidiyo ta manhajar Zoom a yau Asabar.

An yi taron ne da nufin lalubo hanyoyin magance matsalar fyade da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.

Gwamnan ya ce cikin harshen Turanci wanda da shi aka gudanar da taron “Remove the tools”, wato a cire kayan aikin.

Sannan gwamnan ya ce a jiharsa ta Kaduna an samu karuwar fyade inda aka yi wa mutum 485 cikin kankanin lokaci a baya-bayan nan, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *Back to top button