Labarai

Sarkin Musulmi ya bayyana ma Musulmai inda zasu gudanar da sallar Idin bana

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa a Masallatan Juma’a za’a gudanar da sallar Idi a bana a jahar Sakkwato da kewaye.

Gidan rediyon muryar Amurka, VOA ta ruwaito hakan na nufin Musulmai za su gudanar da sallar Idi ba kamar yadda suka saba yi a manyan filaye ba, saboda annobar Coronavirus.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin ganawa da wasu shuwagabannin al’ummar jahar Sakkwato da suka kai masa ziyara dangane da batun sallar Idin bana.

Sarkin Musulmi a Idi Hoto: The Defender

Sarkin ya shaida ma wakilan cewa ba a dauki wannan mataki don hana jama’a sallar Idi ba, illa an yi ne don kare lafiyarsu, don haka ya nemi jama’a su yi biyayya ga wannan tsarin.

Bugu da kari, Sarkin ya bayyana cewa ba ma jahar Sakkwato kadai ba, jahohi da dama ma haka zasu dabbaka tsarin gudanar da sallar Idi a Masallatan Juma’a.

Daga karshe kuma ya nemi shuwagabannin gwamnatoci a matakai daban daban da su cigaba da kokarin da suke yi don ganin an ga bayan annobar cutar Coronavirus.

A yanzu dai ra’ayi ya bambanta tsakanin jama’an jahar Sakkwato game da wannan umarni, inda wasu ke ganin matakin ya yi daidai, wasu kuma suna ganin bai dace ba.

A wani labari kuma, Gwamnatin Saudiyya ta umarci jama’an kasar su gudanar da sallar Idin bana a gidajensu bayan samun fatawar majalisar malamai ta kasar.

BBC Hausa ta ruwaito shugaban majalisar Malaman kasar dake bada fatawa, Abdul Aziz Asheikh ne ya sanar da haka, inda yace ya halasta a yi Idi a gida duba da annobar da ake fama da ita.

Haka zalika Shehin Malamin ya ce ita ma zakkar fidda kai ba sai an bi gida gida ba duba da dokar zaman gida da aka sanya, amma za a iya bayarwa ta hannun kungiyoyin bayar da agaji.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?