Friday, 22 May 2020
Mun Kori Duk Ma’aikacin Asibitin Da Ya Ki Zuwa Aiki, Saboda Ya Shiga Yajin Aiki A Jihar Kaduna, Cewar Gwamna El-Rufai

Home Mun Kori Duk Ma’aikacin Asibitin Da Ya Ki Zuwa Aiki, Saboda Ya Shiga Yajin Aiki A Jihar Kaduna, Cewar Gwamna El-Rufai
Ku Tura A Social Media

Daga Comr Abba Sani Pantami

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gargadi ma’aikatan asibitocin jihar, da ya hada da nas-nas da likitoci cewa duk wanda ya biye wa kungiyar likitoci reshen jihar ya ki zuwa aiki, ya dauka tamkar ya yi sallama da aikin ne Kwata-kwata.

A takarda da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis wanda Muyiwa Adekeye ya saka wa hannu gwamna Nasir El-Rufai ya ce gwamnati ta na dukkan abinda ya Dace domin kula da ma’aikatanta.

Kira da a fara yajin aiki a wannan yanayi na Korona, goga wa gwamnati kashin kaji kawai amma Babu dalilin yin haka.

Duk ma’aikacin da yake son ya ci gaba da aiki da gwamnatin Kaduna ya je Inda yake aiki ya saka hannu a rajista.

Wadanda kuma ba su son yin aikin kada su kuskura su ce za so datse kofofin asibitoci, ko wuraren kiwon lafiya. Ko kuma su ce za su muzantawa wadanda suka zo aiki. Yin haka karya doka ne.

Source: facebook/Rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: