Labarai

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Bai Ce Kada A Yi Sallar Idi Ba Ko Ayi A Gidaje Ba ( A cikin Hoto)

Mai Alfarma ya yi kira ga dukkanin garuruwan da Gwamnoninsu da Sarakunansu suka amince da Za’ayi sallar ta Idi to a guji cunkoson Jama’a domin gudun wannan cunkoso a bi matakai kamar haka;
1. A yi Sallolin a Masallatan Jumu’a ba a bayan gari ba. Kamar yadda aka saba.
2. Addinin Musulunci ya yarda da mata da kananan yara su je Masallaci, amma domin rage cunkoso a guji zuwan mata da kananan yara Masallacin domin maslaha.
Wannan shine shawarar da Kwamiti suka baiwa Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma ya amince da haka.
Haka kuma Mai Alfama ya bukaci duk garin da Gwamnatocinsu ba su yarda da a yi taron sallar ba, to su yi hakuri sucyi Sallarsu a gida tare da Iyalansu domin addini bai hana haka ba.
Jamilu Sani Rarah
Thu 21-05-2020

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?