Addini

Kotu Ta Hana Jami’an Tsaro Sake Kama Ko Kuma Muzgunawa Malamin Addini A Sokoto

Mayu 28-2020
Babbar kotu a jihar Sakkwato ta dakatar da shugaban ‘yan sanda na ‘kasa, kwamishinan ‘yan sanda na jahar Kaduna tare da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Sakkwato daga sake wani yun’kurin kama wani babban malami da ake zargi da wasu laifuka wato Malam Bello Aliyu Yabo.
Umrnin na kotun ya bayyana ne a kafar ‘Newsdiaryonline’ a ranar Laraba kamar haka: “Umurnin wucin gadi da kotu ta bayar, yana hani tare da dakatar da wanda ya ke ‘kara shi da kansa ko wakilinsa ko kuma wani wanda ya ke aiki a ‘kar’kashinsa sake wani yun’kurin gayyata, kamawa, bincike ko kuma shiga a cikin wani sha’anin da ya shafi wanda ake ‘kara ko wakilinsa dangani da ‘karar da  gwamnatin jihar Kaduna ta shigar akan wanda ake ‘kara, kafin kotu ta saurari al’amarin tare da yanke hunkuci ‘karar mai Lamba SS/M.211/2020 wanda yanzu haka tana a gaban wannan kuto mai girma”

Alkali Mohammed Muhammed na kotun ya ‘kara da cewa ” ‘Karar da aka gabatar mai Lamba M.211/2020 tana a gaban kotu kuma an saka 11/06/2020 domin fara saurarenta”
Idan ba’a manta ba dai Shaihin Malamin na jihar Sakkwato an kama shi ne sanadiyyar yin wasu maganganu masu ‘kunshe da 6atanci tare da ‘kalubalantar jihar Kaduna akan dokar han fitar da ta sanya. Wannan dalilin da ya sa gwamnatin jihar Kaduna ta ‘dauki matakin kama shi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button