Addini

Hukuncin Azumin Matar Da Ta Sanya Hannu A Gabanta (Farji)

TAMBAYA TA 2746
*******************
Assalamu alaikum malam Dan Allah inaso a amsa min tambaya, a xauren fiqhu na dauki numbar Nan, inada infection ne toh Ina yawan discharge daxu Ina tsarki xanyi sallah sai saka Dan yatsa na kwaso abun, toh Kuma shine nake kokwanto Dan Allah ya matsayin aximina yake, bansan yanda ake rubuta tambaya ba ta Facebook shine na dauki numbar na turo, Dan Allah a amsamin malam sbda Ina cikin kokwanto tun dazu na tambayi mijina yace wallahi shima Bai sani ba.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah.

Azuminki bai karye ba, tunda kinyi hakan ne da niyyar fitar da dattin fake makalewa awajen. Kuma abinda ya fita daga jikkn naki ba maniyyi bane, hasali ma chuta ce. (Allah shi baki lafiya).

Ga wata fa’ida zan kwatanta miki :

Ki nemi habbur Rashan ki nikashi sosai, sannan ki rika tafasa cokali biyu na garin acikin ruwa, sai ki juye acikin baho ko wata babbar roba. Ki surkashi ka’dan sannan ki shiga cikinsa ki zauna tsawon minti 10.

Sannan ki rika zuba garin nasa cikkn karamin cokali guda (1 teaspoon) acikin nono ko kindirmo kina sha kullum sau 1.

In sha Allahu zaki samu waraka.

WALLAHU A’ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (27/09/1441 20/05/2020).

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button