Addini

Hanyoyi Guda Goma Sha Hudu 14 Da Zaka Bi Domin Gujewa Aikata Zina

Babban Maganin da zai hanaka yin Zina, shine:

1. Tsayuwa abisa tafarkin Allah da Manzonsa (saww) da gaskiya.

2. Cikakken jin tsoron Allah afili da boye. Tare da yin abota da mutanen kirki.

3. Kulawa da yin Sallah akan lokaci, kuma acikin Jam’I. Tare da neman ilimin sanin Sallar.

4. Zikirin Allah safe da yamma tare da neman tsarinsa daga Sharrin Shaitan ako yaushe.

5. Tuna girman Allah da kuma Kusancinsa gareka/gareki.
Yana tare dakai/dake alokacin da kuke aikata wannan Kaba’irar

6.Tunowa da girman azabar da Allah ya tanadar ma MAZINATA alahira. Kuma yadda bakaji kunyar sa’ba masa ba, shima ba zaiji nauyin azabtar dakai ba. (Allah shi kiyayemu).

7. Tunowa shaitan da mummunan kaidinsa da yake Qullawa domin hallakar da ‘Yan Adam. Tare da Qauracewa duk saurayi da kika tabbatar fasiqi ne, ko budurwar da ka tabbatar fasika ce.

8. Gujewa kadaituwa da duk wata Matar da ba Muharramarka ba/ko Namijin da ba Muharraminki ba. Koda kuwa ya biya sadakinki ai ba’a daura muku aure ba, Kuma baki zama matarsa ba. Don haka har yanzu jikinki bai zama halal dinsa ba. Kada ki yarda ya ta’ba koda yatsan hannunki.

9. Kaucewa kalle-kallen fina-finan batsa. Ko kuma wakoki da hotunan batsa ko litattafan soyayya. Ko duk abinda zai janyo motsawar sha’awa.

10. Kaucewa abota ko Qawance da duk wani saurayi Mazinaci ko budurwa Mazinaciya.

11. Ka tuna cewar Wannan da zaka yi zinar da ita:  ‘diyar wani ce, Qanwar wani ce, Yayar wani ce. Watarana kuma zata zama Uwar wani.

To yadda kayi Zina da ita, kaima sai anyi Zina da Uwarka, ko Qanwarka, ko yayarka, ko ‘yar cikinka wacce ka haifa.

12. Addu’ar neman tsari daga Miyagun ayyuka, da mummunan tunani.

“Allahumma inni a’uzu bika min Munkaratil Akhlaaqi wal Af’aali wal Ahwa’I.”

13. Daga karshe kuma ka tuna cewa zaka iya kamuwa da wata mummunar chutar da zata zamanto ajalinka.. Kuma koda baka kamu da Chutar zahiri ba, Wallahi in dai ka aikata zina sai chutar Munafurci da Fasikanci da fajirci ta shiga zuciyarka, zuciyarka ta kekashe.
14. Tuno ranar da za’a tsayar da kai agaban Allah, a ranar taron Alqiyamah.. Ga iyayenka da Kakanninka, ga ‘Ya’yanka har Jikokinka da jikokin-Jikokinka.. agabansu al’aurarka zata bada shaidar cewa Ka aikata abu kaza da ita arana kaza, awaje Kaza.. Mala’iku kuma zasu kawoshi arubuce, sannan  Allah zai nuna maka hotonka (kamar bidiyo) gaka nan alokacin da kake aikatawa.
Fatan Zauren Fiqhu shine Allah shi kiyayemu baki daya daga wannan mummunan aiki. Wadanda kuma shaitan ya riga ya rudesu, to Allah yasa wannan rubutun ya zama dalilin tubansu, Allah yasa mu rabauta baki dayanmu ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 08157968686  (18-04-2017)

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button