Labarai

DOKAR CORONA: Martani Mai Zafi Da Addinin Ake Yaki A Kaduna Ba Corona Ba ~ Cewar Sheikh Bello Yabo

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Shehin Malamin na jihar Sokoto a wani karatu da ya gabatar ya kalubalanci Gwamnan jihar Kaduna da cewa ba yaki yake da cutar corona virus ba illa yana fada da addinni ne.

Ya ce “ya za a yi a ware ranakun zuwa kasuwa sau biyu a sati amma a ki ware ranar zuwa masallaci?

“Har ta kai ga malamai a jahar Kaduna sun rubuta takarda na cewar a taimaka musu da su yi sallar Juma’a ko da na minti 30 ne.
Sai ya turo wata mai guntun gyale ta zo ta ce musu idan dai akan sai an ba su damar sun yi sallah ne maganar banza suke yi. Gwamnatin ba za ta bari a yi sallar Juma’a ba”.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button