Fadakarwa

Dan Allah ka Karanta! Labari Mai Ban Tsausayi, Al’ajabi Da Firgita Dauke Da Darasi Ga Dukkan Ɗan Adam Mace Da Namiji

 

Daga Haji Shehu

Wannan daki da kuke kallo dakin wani attajirin mutum ne wanda ya rayu cikin walwala tare da iyalan sa, ya kasance mutum mai kulawa da dukkanin dawainiyar gidansa tare da biyawa iyalansa dukkanin bukata komi tsadar ta.

Haka rayuwarsa da ta yaransa suka kasance cikin daula da rayuwa mai matukar inganci har zuwa lokacin da tsufa ya riske shi ya kuma yi ritaya daga aiki, inda ya dawo gida domin cigaba da rayuwa bayan ritaya. Duk da cewar bayan yin ritaya daga aiki rayuwa tana daukar sabon salo, hakan baisa ya rage wani abu daga cikin walwalar gidansa ba.

Duk abunda yaransa keso komi tsadan abun yana cire kudi domin yi musu saboda soyayyar da yake musu.

Kwanci tashi yaransa suka girma har ta kai ga sunyi aure a lokacin da tsufa ya kamashi sosai,  sannan ya kamu da ciwon hawan jini wanda ya janyo masa shanyewar barin jiki, da kuma ciwon tsufa.

Bayan yaran sunyi aure, sai suka kebe shi a gefe guda cikin gidan inda suka nemo mutumin da zaike kulawa dashi suna biyanshi duk wata, ga mahaifiyar su ta mutu. Wani lokaci bayan aure sai yaran suka shirya tafiya zuwa wani waje domin cin angoncin tare da iyalansu.

Nan suka damka duk wani kayan bukata ga mai kula da mahaifinsu tare da makullin dakin da suka killace mahaifin da zummar bayan watanni biyu zuwa uku zasu dawo daga hutun cin angoncin, ashe basu san rabuwar kenan ba.

Bayan sun tafi cin angonci, mai kulawa da mahaifin nasu ya fita kasuwa domin sayayya, kwatsam sai mota ta bugeshi wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar shi. Su kuma yaransa suna can suna holewarsu da tunanin cewar ana kulawa da tsohon su da suka gagara zama dashi a lokacin da yake tsananin bukatar su.

Tsofo yana daki a killace, ga jinya ga tsufa, ga kuma yunwa, haka yayita rayuwa har ya mutu, gawarsa ta rube tayi tsutsa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comRelated Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button