Uncategorized

Shan Shayi mai zafi sosai yana kara jawo ciwon Daji (Cancer) – Masana

Mutane dayawa na fara shan shayi bayan tashin su da safiya. Sai dai wani sabon bincike ya nuna cewa masu kurbarshi da zafi sosai na iya janyo musu ciwon Dajin makwogwaro (Esophageal Cancer)

Masana sun binciko cewa masu shan shayi da zafin daya kai digiri 60 bisa ma’aunin Salshius (60°C) tare da shan shayin dayawa, wanda adadinshi yakai manyan kofina guda 2, sunfi damar daukan ciwon daji da kaso 90 bisa 100, akan wadanda basa shan shayin da zafi da kuma wadanda suke shanshi da sanyi madai-daici.

Masanan sun tabbatar da haka ne bayan da suka gudanar da bincike akan mutum Dubu Hamsin (50,000) a birnin Golestan dake arewacin kasar Iran.

Da yake bayani a gaban Cibiyar Cancer ta kasar Amurka, Dr. Farhad Islami yayi kira ga masu shan shayi da zafi, su rika bari ya huce kafin su sha.

“Mutane dayawa sun son shan shayi, coffee da sauran abubuwan sha masu zafi. Bincikenmu ya nuna mana cewa shan shayi mai zafin gaske yana kara janyo ciwon Daji (Cancer), shiyasa muke kira ga mutane da su rika bari abin shan ya huce kafin su sha.”

An wallafa wannan binciken a Jaridar Cancer ta Duniya, ranar Laraba 20/03/2019.

Cancer dake kama makwogwaro na daya daga cikin nau’in Cancer dake da babbar illa, hukumar dake kula da bincike akan Cancer ta bayyana cewa tana kashe mutane kimanin dubu dari hudu (400,000) a kowacce shekara.

Daga Jaridar News World Hausa wannan Jaridar za taci Gaba Da kawo muku Ingantattun labaran Cikin Gida Nigeria da wasu sassan a fadin Duniya sannan zata Rika kawo muku Shirye Shirye da Tunatarwa da wa,azantarwa Akan Addinin Musulunci sannan Ga mai Bukatar a tallata masa Hajarsa zai Iya Tuntubarmu muna Tallata Haja a farashi mai sauki

Don Allah Kuyi Share Domin mutane sun Amfana

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button