Labarai

Masha Allah ! Korafi Zuwa Ga Baba Buhari Mai Gaskiya – Datti Asaalafy

Ina yiwa Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya fatan alheri

Bayan haka Maigirma shugaban Kasa talakawanka suna korafi cewa tallafin da gwamnatin Nigeria take rabawa domin a saukakawa al’ummah saboda halin kunci da ake ciki a dalilin Coronavirus tallafin bai isa zuwa garesu

Ko ni nan Datti Assalafiy a labarai da hotuna nake gani wakilanka suna raba tallafi, amma ban taba ganin tallafin da idona ba, kuma a gaskiya talakawa suna kuka sosai musamman a jihohin da aka haramta musu fita neman abincin da zasuci su rayu

Shugaba Buhari ya kamata ka saka ido sosai domin hakkin talakawan Nigeria ya isa garesu lungu da sako, a kuma cire ra’ayin banbancin jam’iyya na siyasa, sanin kanka ne cewa akwai mahinta kuma azzalumai maciya  amana da suke maka zagon kasa

Allah Ka taimaki shugaba Buhari Ka bashi ikon aikata daidai Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?