Kannywood

Dalilin Da Yasa Ba’ a Jin Wakokina A Cikin Fina Finai – Hamisu Breaker

A Yanzu dai za a iya cewa a masana’antar fina-finai ta Kannywood babu wani mawaki da ya ke tashe kamar Hamisu Breaker Dorayi, domin kuwa a yanzu shi ne tauraruwar sa ta ke haskawa, dangane da haka ne a ke ganin mawakin ya sha gaban abokan sana’ar sa ta fuskar dumbun masoya, sai dai duk da tashen sa mawakin ya zo da wani Salo da ya bamban ta da sauran mawakan da ke cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood, domin kuwa, kusan duk mawakin da ya yi tashe a cikin harkar za ka ga wakokin fim ne su ka daga shi, amma shi mawaki Hamisu Breaker sam ba a cika saka wakokin sa ma a cikin fim  ba ko me ya sa hakan? Northflix na wallafa

Domin jin hanzarin sa game da hakan wakilin mu ya tattauna da shi, amma da farko ya fara da tarihin rayuwar sa kamar haka.

“Suna na Hamisu Sa’id, Yusif wanda a ka fi sa ni da Hamisu Breaker. An haife ni a unguwar Dorayi karama, Unguwar Bello. Na yi firamare a Dorayi karama Sakandare a Dorayi Babba, daga nan na dakata, amma ina da burin ci gaba da karatu da yardar Allah”.

Dangane da yadda ya samu kan sa kuwa a cikin harkar waka cewa ya yi.

“Tun ina karami na ke da sha’ awar waka har na je makarantar Islamiyya, daga nan dai shi ne asalin samun kai na a cikin harkar waka zuwa yanzu”.

Da ya ke Hamisu Breaker ya yi wakoki da yawa ko wacce wakar ya fi so a cikin wakokin sa?
“Wakar da na fi so ita ce (Ke ce) wakar da na ke cewa ‘A duniya ke ki ka zam farin cikina. idan  ba kya nan wa za na bai wa kauna”.

Duk da cewar Hamisu Breaker mawki ne a masana’antar fina-finai ta Kannywood, sai dai ba a cika jin wakokin ka a cikin fim ba ko me ya sa?

“Gaskiya ba a cika ji na ba, dalili na farko shi ne yanayin sakon da na zo da shi ba irin na fim ba ne, kasancewar yawancin fim waka a na sanya maza da mata ne, ni kuma nimiji kawai. Kuma na lura da yadda za a kawo wani sauyi, kuma Allah ne ke yin komai, kuma ina godiya ga Allah domin kwarin gwiwar da na ke da shi bai fadi a banza ba, domin jama’a sun karba kuma daman su a ke so su karba, wannan ya sa ban raja’a kan wakokin fim ba ko da a ka fara jina, domin mutane sun fi son juna a irin wakokin da na ke yi, kuma za ka ga yawancin su ma ba su da muhalli a fim”.

Da ya ke Hamisu Breaker ya samu daukaka, ya na fuskantar wata matsala?

“Bayan nasara da daukaka na ga wasu kalubalen da dama. Shi ma bamabancin ra’ayi ne na mutane, wannan ya na son kaza wancan ya na son kaza. Amma shi ma din kasancewar duk masoya ne ba sai na bayyana ba, ba zan so abun da zai shafi masoya na ba”. A cewar Hamisu Breaker.

Daga karshe ya yi fatan alheri ga dubum masoyan sa da su ke nuna masa kauna a kowanne lokaci.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?