Kannywood

Adam A Zango ba dan Kannywood ba ne -Alhassan Kwalle

Shugaban kungiyar jarumai ta kasa wato (Hausa Actors Guild of Nigeria) Alhassan Kwalle, ya ce mutane su daina kallon jarumi Adam A Zango a matsayin dan kungiyar domin kuwa har yanzu ba su san da zaman sa ba duk da maganganun da a ke ta yadawa cewar jarumin ya dawo Kannywood.

Alhassan Kwalle, ya kuma ce jarumin bai yi rijista da kungiyar su ba har zuwa yanzu domin haka ba sa daukar sa a matsayin mamba a cikin su.

Ya ce” Har zuwa yanzu dai Adam A Zango ba dan Kannywood ba ne, domin har yanzu bai yi rajista da kungiyar jarumai ta Hausa Actors Guild of Nigeria ba, wadda kuma a cikin ta ne jaruman Kannywood su ke, kuma da ita hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta yarda, duk wani dan kungiyar shi ne cikakken jarumin da hukumar ta yarda ya gudanar da aikin sa, amma shi Adam A Zango ba shi da rijista da mu har zuwa yanzu”. Inji Alhassan.

Da mu ka tambaye shi ko ba ya ganin Adam A Zango din ya je ya yi rijista da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano?

Sai ya ce” To ni dai ban sa ni ba, domin a ka’ida duk wani jarumi da hukumar tace fina-finai za ta yi wa rijista, sai ya zo ya bi ta karkashin kungiyar ‘yan fim a bangaren da zai yi aiki, kamar darakta, sai ya je ya yi rijista da kungiyar daraktoci, haka furodusa, domin haka shi ma Adam A Zango, a matsayin sa na jarumi, dole sai ya na da rijista da kungiyar jarumai sannan hukumar tace fina-finai ta jihar Kano za ta yi masa rijista, hakan dokar ta tsara, kuma har yanzu ba canja wa a ka yi ba, saboda haka Adam A Zango ba dan Kannywood ba ne kuma har yanzu ba shi da wani hurumi da doka ta ba shi ya gudanar da duk wani aiki na fim a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood”. A cewar Alhassan Kwalle.

Alhassan Kwalle ya dai bayyana hakan ne ga wakilin mu dangane da furucin da shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano, Isma’ila Na Abba Afakallahu ya bayyana cewa har yanzu jarumi Adam A Zango bai yi rijista da kungiyar su baShugaban kungiyar jarumai ta kasa wato (Hausa Actors Guild of Nigeria) Alhassan Kwalle, ya ce mutane su daina kallon jarumi Adam A Zango a matsayin dan kungiyar domin kuwa har yanzu ba su san da zaman sa ba duk da maganganun da a ke ta yadawa cewar jarumin ya dawo Kannywood.

Alhassan Kwalle, ya kuma ce jarumin bai yi rijista da kungiyar su ba har zuwa yanzu domin haka ba sa daukar sa a matsayin mamba a cikin su.

Ya ce” Har zuwa yanzu dai Adam A Zango ba dan Kannywood ba ne, domin har yanzu bai yi rajista da kungiyar jarumai ta Hausa Actors Guild of Nigeria ba, wadda kuma a cikin ta ne jaruman Kannywood su ke, kuma da ita hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta yarda, duk wani dan kungiyar shi ne cikakken jarumin da hukumar ta yarda ya gudanar da aikin sa, amma shi Adam A Zango ba shi da rijista da mu har zuwa yanzu”. Inji Alhassan.

Da mu ka tambaye shi ko ba ya ganin Adam A Zango din ya je ya yi rijista da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano?

Sai ya ce” To ni dai ban sa ni ba, domin a ka’ida duk wani jarumi da hukumar tace fina-finai za ta yi wa rijista, sai ya zo ya bi ta karkashin kungiyar ‘yan fim a bangaren da zai yi aiki, kamar darakta, sai ya je ya yi rijista da kungiyar daraktoci, haka furodusa, domin haka shi ma Adam A Zango, a matsayin sa na jarumi, dole sai ya na da rijista da kungiyar jarumai sannan hukumar tace fina-finai ta jihar Kano za ta yi masa rijista, hakan dokar ta tsara, kuma har yanzu ba canja wa a ka yi ba, saboda haka Adam A Zango ba dan Kannywood ba ne kuma har yanzu ba shi da wani hurumi da doka ta ba shi ya gudanar da duk wani aiki na fim a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood”. A cewar Alhassan Kwalle.

Alhassan Kwalle ya dai bayyana hakan ne ga wakilin mu dangane da furucin da shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano, Isma’ila Na Abba Afakallahu ya bayyana cewa har yanzu jarumi Adam A Zango bai yi rijista da kungiyar su ba

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button