Monday, 2 March 2020
Yadda na tsinci kai na a harkar fim -Fatima Fulani

Home Yadda na tsinci kai na a harkar fim -Fatima Fulani
Ku Tura A Social Media
A kullum masana'antar fina-finai ta Kannywood ta na samun sabbin jarumai da su ke  shigowa cikin ta maza da mata, domin yadda su ke sha'awar harkar wanda a kullum masana'antar ba ta rabuwa da bakuwar fuska a cikin ta.

Fatima Muhammad Fulani, sabuwar jaruma ce da ta shigo masana'antar a cikin 'yan kwanakin nan, domin kuwa ita ma ta jarraba sa'ar ta kamar yadda sauran jarumai ke yi, ko za ta iya kasancewa babbar jaruma kamar yadda wasu su ka shigo ciki su ka yi fice harma a ka san su a duniya.

Jarumar, 'yar shekaru 20 da haihuwa, an haife ta ne a garin Kano, kuma a nan ta yi karatun ta na firamare da na sakandare, kuma a halin yanzu ta na ci gaba da karatun NCE a kwalejin Sa' adatu Rimi.

Domin jin dalilin ta na shigowa harkar fim da kuma yadda ta samu harkar, wakilin mu ya tattauna da ita inda ta fara bada labari da cewar. "To ni dai zan iya cewa harkar fim na shigo ta ne domin sha'awa da kuma fadakarwa, saboda yadda na ga jarumai su na bayar da gudummawa wajen wayar da kan al'umma, domin haka ne ma na ga zan iya bayar da tawa gudummawar. Amma dai daman tun tuni ina da sha'awar na shigo saboda karatu, domin haka ko a gida ma ba za a bar ni ba a lokacin, sai yanzu ne na samu damar shigowa, domin yanzu ma ban fi wata biyu zuwa uku ba".

Ko ya ya ki ka yi wajen shigowa cikin harkar?

"To gaskiya daman akwai Abdullahi Aji Papa, shi ne mu ke maganar da shi ya ke cewa da ni ya kamata na yi harkar domin za ta dace da ni, to kuma da ya tashi yin fim sai ya saka ni a ciki. A lokacin ma ni abun wasa na dauke shi, amma dai da Allah ya sa zan yi sai kawai na je na fara".

Ko ya ya ki ka ji a lokacin da a ka saka ki a cikin fim?

"To gaskiya abun ya zo min da ba zata, domin sai na ji kamar ba zan iya ba, amma dai a haka na daure har na yi abun da a ka saka ni, amma dai da na zo yin na biyu to sai abun ya fi na baya, domin sai na ji har na saba, har wadanda su ke wajen ma sai da su ka yi mamaki na saboda kokarin da su ka ce na yi".

Ko wadan ne fim ki ka yi daga shigowar ki zuwa yanzu?

"E to na fara ne, domin yanzu fim din da na yi bayan na yi na farko shi ne Dan Malam, wanda mu ka yi da Sadik Sani Sadik na fito a matsayin kanwar sa, sai kuma so da so, shi kuma na fito a matsayin budurwa, daga nan kuma sai wakoki da na yi".

To ko ya ya ki ka samu harkar fim din?

"To gaskiya yadda na samu harkar fim din ba kamar yadda na ke jin ta ba kafin na shigo, na san dai komai na rayuwa za ka samu mutane nagari kuma akwai wadanda ba na gari ba, domin haka ni dai yadda na samu harkar fim abun ya burgeni".

Ko wanne buri ki ke so ki cimma a cikin masana'antar?

" To babban buri na dai kamar yadda na fada maka a baya shi ne fadakarwa, domin haka ina fatan ta silar fim din da zan yi, mutane su fadaka daga abubuwan da su ke marasa kyau, domin haka na ke fatan na zama babbar jarumar da za a sanni a duniya ta hanyar wayar da kan jama'a".

Ko Fatima ta taba yin aure?

"To gaskiya ban taba yin aure ba sai nan gaba, kuma ina fatan yadda na shiga harkar nan lafiya na fita lafiya, yadda zan samu na yi aure cikin kwanciyar hankali".

Daga karshe wacce shawara za ki baiwa masu son shigowa harkar fim? "Ni dai shawarar da zan ba su ita ce su shigo da kyakyawar niyya, shi ne zai sa su kare mutuncin su, kuma su dauka fadakarwa su ka zo yi ba wai su zubar da mutuncin su ba, domin duk in da mutum ya kare mutuncin sa to kimar sa ba za ta taba zubewa ba". A cewar Fatima. Northflix Na ruwaito.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: