Monday, 16 March 2020
Nafisa Abdullahi Tayi Bayanin Yanda Ta Fara Haduwa Da Ali Nuhu

Home Nafisa Abdullahi Tayi Bayanin Yanda Ta Fara Haduwa Da Ali Nuhu
Ku Tura A Social Media
Tauraruwar fina-finan Hausa,Nafisa Abdullahi a sakon data aikewa Ali Nuhu na murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta bayyana yanda suka haduu.

A cikin sakon data saka a shafukanta na sada zumunta,Nafisa ta bayyana cewa, sun hadu karin farko ita da Ali Nuhu a wajan hada fim din (Haaja), ta kara da cewa a karin farko da ya ganta, bata san abinda ya gani ba, yace zai shirya mata fim.

Nafisa ta Kara da cewa daga nanne Ali ya shirya mata shirin fim din Sai Wata Rana kuma duk da yake cewa ita sabuwar Jarumace, ya biyata kudi masu yawa.

A karshe dai Nafisa ta taya Ali Nuhu murnar zagayowar Ranar Haihuwarsa.


View this post on Instagram

A post shared by NAFISAT ABDULLAHI (@nafeesat_official) on

Share this


Author: verified_user

1 comment:

  1. Assalamu Alaikum Sunana Usman Ibrahim Mamallakin Channel din Duniyar Kannywood. please inason magana dakai Ga WhatsApp No. 07063865041

    ReplyDelete