Saturday, 21 March 2020
Mutum 51 kacal Adam Zango ya ke hulda da su a shafin Instgram –Adam Zango

Home Mutum 51 kacal Adam Zango ya ke hulda da su a shafin Instgram –Adam Zango
Ku Tura A Social Media
Shahararren mawakin Hausa, kuma tsohon jarumi a masana'antar Kannywood, Adam A Zango, ya fara bin mutane 31 kacal wanda ya zaba ya kuma yi mu'amala da su a shafin sa na sada zumunta wato Instagram.

Adam A Zango mawakin gambara wato Hip pop, ya fara bin mutanen ne a shafin sa na Instagram a cikin ‘yan kwanakin nan, samakon a baya sai da ya dai na hulda da dukannin abokan sa a cikin shafin sakamakon goge su da ya yi.
A dai watannin baya ne dai jarumin ya goge sunayen duk wadanda ya ke bi a shafin sa na Instgram ciki kuwa harda matar sa da kuma aminin sa.

A na zargin hakan dai ya samo asali ne sakamakon takun saka da ya ke yi da wasu abokan aikin sa da kuma takunkumi da hukumar tace fina-finai da Dab'i ta jihar Kano ta sa wa jarumin wanda idan mai sauraro bai manta ba, ko a baya sai da jarumin ya yi yunkurin shigowa jihar Kano domin ya kalli fim din Mati a Zazzau amma abun ya ci tura, sakamakon samun labarin da Adam A Zangon ya yi na cewa hukumar na farautar sa.

Sai dai kuma a cikin 'yan kwanakin nan dai a ka ga jarumin ya na sanya hotunan wasu jarumai daban-daban a shafin sa na Instagram ba tare da rubuta komai ba a kai. A cikin jaruman da ya ke sanya hotunan na su sun hadar da Falalu A Dorayi, Ali Jita, Rahama Sadau, Umar M Shareef, Baban Chinedu da kuma Zee Pretty da dai sauran su.

To sai dai abun tambayar shi ne ko hakan na nufin jarumin ya fara shiryawa da abokan aikin na sa ne? Ko kuma zai dawo cikin masana'antar Kannywood domin ci gaba da harkar sa kamar yadda ya saba a baya?

Share this


Author: verified_user

0 Comments: