Kannywood

Gutsiri tsoma da fushi ya fi komai ci mun tuwo a kwarya -Rikadawa

Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood, Rabi’u Rikadawa ya bayyana cewa fushi da fushin wani a matsayin abun da yafi komai ci mai tuwo a kwarya a tafiyar Kannywood.

Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin da su ke tattaunawa da wakiliyar mu dangane da abubuwan da suke faruwa a masana’antar Kannywood, inda kuma wakilin namu yake tambayar sa kamar haka:

Matsayinka na jarumin da a ka dama dashi sosai a masana’antar Kannywood ko kuma ince a ke damawa da shi a masana’antar me za ka ce dangane da gutsiri tsoma da baya karewa a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood?

Jarumin ya ce “Gutsiri tsoma babu inda ba a yin ta, sai dai har kullum mu da yake a bakin duniya muke, shi ya sa tamu idan a ka yi tafi zama abun surutu, amma dai a kullum ya kamata a ce mutum idan har yasan inda ya fadi abu zai tada hankali ko kuma baka da tabbas a kai, to ka yi shiru bai kamata ka fade shi ba. Wannan ko ina a na samun haka sai dai kawai dai fatan mu mutane su rinka kiyayewa domin babu amfani na tada wata rigima, sai dai kuma mu ma mutane ne kamar kowa, kuma ko wane akwai daga inda ya fito da kuma irin tarbiyar da ya samu, saboda haka ba ka isa ka ce kowa sai ka saita shi yadda ka ke so ba”.

Amma ya ka ke ganin tafiyar Kannywood, ina nufin kai a ganinka Kannywood gaba ta ke yi ko sake tabarbarewa ta ke yi?

“Babu maganar tabarbarewa gaskiya, Kannywood gaba ta ke yi, domin da ba a ci gaba da ba a kawo wannan lokacin ba, sannan idan ki ka duba fina-finan mu na da da na yanzu ai akwai banbanci, hatta da yanayin labari da na’urar daukar hoto duk an samu ci gaba, domin haka maganar tabarbarewa ma ba ta taso ba”.

Me yafi ci maka tuwo a kwarya a tafiyar da Kannywood ta ke a yanzu?

“Babu abun da yafi ci mun tuwo a kwarya a tafiyar Kannywood irin gutsiri tsomar da a ke yi, domin ya samu babban muhalli a Kannywood yanzu haka, kuma ba na son ta har ga Allah, sannan kuma fushi da fushin wani, mutum haka kawai ya zauna ya dauki fushi da fushin wani shima ba na so, mutum ba shi a ka taba ba, ba komai ba, wai an taba wani na shi sai ya zauna ya maida maganar wata a ba, ya yi ta yi ya na  nanatawa ya na korafi da batanci a kan abun da bai shafeshi ba, wannan babban kuskure ne, sannan abu na uku shi ne rashin sirri da muke yi, a ce mutum daidai da kaza idan ya na ci sai ya dauki hoto ya dora a kan shafin sada zumunta, bare a ce ya samu wasu ‘yan kudi sai dai in bai gansu a daure ba, yanzu zai ta faman yadawa babu kakkautawa, wannan duk shirmene, sana’a ka ke kuma kowa ya na da tashi, kuma ya na da irin wadda ya ke yi, ba sai ka fito ka yadawa mutane duk wani motsi na ka ba.

Me ya sa bakanike idan ya na aiki baya daukar hoton wani babban karfe ya saka a soshiya midiya, ko kuma idan a ka kawo babbar mota ya dauka ya saka? Domin haka ya kamata mu san kan mu mu daina wannan shiriritar”. Inji Rikadawa.

Yadda abubuwa su ka koma yanzu kowa ya na sukar dan uwansa ko kuma kowa ya na jiran kiris dan uwansa ya yi wani abu ya soke shi ka na ganin Kannywood za ta daidaita kuwa?

“ Wannan dai magana ce ta tarbiya, ita Kannywood kamar makaranta ce, yadda a ke haduwa domin wannan gidan da can a hadu a waje daya haka Kannywood take, kowa daga gidaje daban-daban ya fito yazo muka hadu a Kannywood, kuma kowa tarbiyyar da ya samu daban, amma duk da haka akwai masu tarbiyar da suna nan a Kannywood din basa cewa komai.Kannywood za ta iya daidaituwa, amma a kullum sai mun zama masu hakuri da kawaici daga irin wadannan surutan da a ke yi”. A cewar Rabi’u Northflix Na ruwaito

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?